Yaya Za A Cimma “Tsaro Tare”? Dandalin Xiangshan Ya Gabatar Da Wasu Tunani
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yaya Za A Cimma “Tsaro tare”? Dandalin Xiangshan Ya Gabatar Da Wasu Tunani

byCGTN Hausa
2 years ago
Tsaro

An rufe taron dandalin tattaunawa kan batun tsaro na Xiangshan karo na 10 a birnin Beijing jiya Talata. Yayin taron, wakilai fiye da 1800 daga kasashe da yankuna da kuma kungiyoyin kasa da kasa sama da 100 sun gudanar da tattaunawa tare da musayar ra’ayoyi bisa taken “Tsaro na bai daya, zaman lafiya mai dorewa”, adadin mahalarta taron da mukamansu duka sun kai wani matsayin da ba a taba gani a da ba.

Yaya za a cimma buri na “tabbatar da tsaro tare”? Ta hanyar tattaunawar da aka yi a dandalin Xiangshan na Beijing, an samu kyakkyawar fahimta.

  • Hausawa ‘Yan Kasuwar Shanu Na Neman Sasantawa Da Gwamnatin Abiya
  • Sin Ta Yi Nasarar Harba Tauraron Dan Adam Na Tianhui-5 

Ko shakka babu, manyan kasashe suna da nauyi da muhimmanci na musamman wajen wanzar da zaman lafiya da tsaron kasa da kasa. A yayin taron, Xanthi Carras, direktar sashen kula da harkokin kasar Sin a ofishin mai ba da taimako ga mataimakin sakataren ma’aikatar tsaron kasar Amurka ta halarci taron a madadin ma’aikatar tsaron kasar Amurka.

Ana sa ran cewa, bangarorin Amurka da Sin za su iya kai zuciya nesa su yi kokarin samar da wani kyakkyawan yanayi, ta yadda za a iya tabbatar da ganin dangantakar dake tsakanin rundunonin soja na kasashen biyu ta samu ci gaba cikin kwanciyar hankali kamar yadda ake fata.

Idan ana son cimma buri na “tabbatar da tsaro tare”, abu mai muhimmanci shi ne tsayawa tsayin daka kan warware sabani da rikici dake kasancewa tsakanin kasa da kasa ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna cikin lumana. A wannan dandalin, an gayyaci wakilan wasu bangarorin da suke yin rikici da juna, kamar wakilan Isra’ila da na kasashen Larabawa, da Rasha da Ukraine don yin tattaunawa da tuntubar juna fuska da fuska.

Har yanzu, wasu manyan kasashen yamma suna bin ra’ayinsu na tabbatar da “cikakken tsaron kansu”, har ma suna bin tunanin yakin cacar baki, da kuma haddasa fito na fito tsakanin bangarori daban daban, da kuma haifar da kalubale mai sarkakiya ga yanayin kasa da kasa. Masana mahalarta taron suna ganin cewa, dandalin Xiangshan ya ba dukkan kasashen yammacin duniya damar sani da kuma fahimtar matsayi da ra’ayoyi daban daban na sauran kasashen duniya. Hakan yana da matukar muhimmanci ga kasashen duniya da su yi kokarin yin hadin gwiwa domin samun nasara tare. (Safiyah Ma)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa
Daga Birnin Sin

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Next Post
Dankwambo Ya Ce Daga Yanzu Gwamnatin Gombe Ta Daina Biyansa Fansho Ya Yafe

Dankwambo Ya Ce Daga Yanzu Gwamnatin Gombe Ta Daina Biyansa Fansho Ya Yafe

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version