CRI Hausa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAGA BIRNIN SIN

Yaya Za A Kawar Da Damuwar Tedros Adhanom Ghebreyesus? Kasar Sin Ta Bada Amsa

by CRI Hausa
January 22, 2021
in DAGA BIRNIN SIN
2 min read
Yaya Za A Kawar Da Damuwar Tedros Adhanom Ghebreyesus? Kasar Sin Ta Bada Amsa
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Bayyanar alluran riga kafin annobar COVID-19 ba shakka labari ne mai kayatarwa, amma akwai tazara tsakanin mawadata da matalauta wajen karbar wannan “maganin cuta”.
Yaya hali mai tsananin yake na rarraba allurar rigakafi a duk duniya? Kuma alluran rigakafi nawa wata kasa mai karancin kudi za ta iya samu? Babban daraktan kungiyar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, a kwanan nan ya bayyana cewa, kasashe masu arziki 49 sun karbi alluran rigakafi sama da miliyan 39, amma wasu kasashen da ba su ci gaba ba, suna da allura 25 kacal. Kafafen yada labarai da dama sun ruwaito cewa, mutane 25 ne kacal a kasar Guinea, ciki har da shugaban kasar, aka yiwa rigakafin.


“Ba miliyan 25 ba, ba 25,000 ba, 25 kacal! Ina so in fada a bayyane cewa, duniyar da muke ciki tana gab da fadawa cikin mummunan halin dabi’a.” Tedros ya nuna damuwa sosai a kan hakan.
Rarraba allurar rigakafi, ya zama aiki na adalci, da ba da fifiko ga mutanen da suka fi bukata a kasashe daban daban, da kuma baiwa mutanen dake a kasashe masu karamin karfi damar samun rigakafi da wuri-wuri. Wannan shi ne ainihin aniyar WHO, don hakan ne kuma sauran hukumomi suka bullo da shirin COVAX.
Amma gaskiyar ita ce: daga samarwa zuwa saye, masu son alluran rigakafi suna karfafa rashin daidaito tsakanin kasashe masu arziki da matalauta.
Ganin yadda annobar ke addabar duniya, bil Adama na bukatar hadin kai ba tare da la’akari da iyakokin kasa ba, don tinkarar yaduwarta. Game da wannan, kasar Sin tana aiki yadda ya kamata.


A yanzu haka, kasashen Chile, UAE, Bahrain, Masar, Jordan, Turkey, Indonesia, Brazil da sauran kasashe sun amince da amfani da alluran rigakafin kasar Sin. Bisa kididdigar da ba a kammala ba, kasashe sama da 40 sun nemi shigar da alluran rigakafi kirar kasar Sin cikin kasashen su. Shugabannin kasashe da dama da suka hada da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip ErdoÄŸan, da shugaban Seychelles Wavel Ramkalawan, da firaministan kasar Jordan Bisher Al Khasawneh, da shugaban Indonesiya Joko Widodo, an yi musu alluran rigakafin kasar Sin a bayyane.
Annobar na yaduwa a duniya, kuma babu wata kasa da za ta iya rayuwa ita kadai. “Ra’ayin son kai kan alluran rigakafi” ba zai iya magance cutar ba, lokaci ya yi da za a hada kai. Wannan magani ne mai amfani don saukaka damuwar Tedros. Kawai bukatar kasashe mafi yawa su gudanar da irin “ayyukan kasar Sin” don yaki da annobar tare. (Mai fassara: Bilkisu)

SendShareTweetShare
Previous Post

Ya Kamata A Yi Kokari Tare Don Dawo Da Raya Dangantakar Dake Tsakanin Sin Da Amurka

Next Post

Xi Ya Jaddada Muhimmancin Aiki Da Dokokin Jam’iyya A Lokacin Aiwatar Da Ajandar Raya Kasa Ta Shekaru 5 Karo Na 14

RelatedPosts

An Cimma Burika 17 Da Aka Tsara Cikin Rahoton Aikin Gwamnati A Shekarar 2020

An Cimma Burika 17 Da Aka Tsara Cikin Rahoton Aikin Gwamnati A Shekarar 2020

by CRI Hausa
21 hours ago
0

Daga CRI Hausa Jiya Talata, gwamnatin kasar Sin ta sanar...

Karya Fure Take Ba Ta ’Ya’Ya

Karya Fure Take Ba Ta ’Ya’Ya

by CRI Hausa
21 hours ago
0

Daga CRI Hausa Da alamu har yanzu Amurka da wasu...

Wakilin Sin Dake MDD Ya Yi Bayani Kan Fasahohin Sin Na Yaki Da Talauci

Wakilin Sin Dake MDD Ya Yi Bayani Kan Fasahohin Sin Na Yaki Da Talauci

by CRI Hausa
21 hours ago
0

Daga CRI Hausa Jiya Talata, wakilin kasar Sin dake MDD...

Next Post
Xi Ya Jaddada Muhimmancin Aiki Da Dokokin Jam’iyya A Lokacin Aiwatar Da Ajandar Raya Kasa Ta Shekaru 5 Karo Na 14

Xi Ya Jaddada Muhimmancin Aiki Da Dokokin Jam’iyya A Lokacin Aiwatar Da Ajandar Raya Kasa Ta Shekaru 5 Karo Na 14

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version