Yayin Da A Ka Buga Gangar Siyasar 2019!

PIC. 4. A PHYSICALLY CHALLENGED VOTER BEING ACCREDITED AT GARKI PRIMARY SCHOOL POLLING UNIT IN ABUJA ON SATURDAY (28/3/15). 1653/28/3/2015/ZI/BJO/NAN

Kusan tun a makon da ya gabata ne a hukumance INEC ya bai wa masu neman mukamin kujerar Shugaban kasa da na majalisun dokoki na tarayya iznin fara yakin neman zabe a dukkan fadin tarayyar Nijeriya. A bisa tanadi na dokokin hukumar zabe ta masa wanda duk yake neman mukamin kujerar Shugaban kasa Yana Iya fara yawan yakin neman zabe domin neman goyon baya.
Tuni wasu masu shiri suka fara, dan kuwa zancen da muke yi tsohon mataimakin Shugaban kasa kuma dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya kaddamar da fara yakin neman zabensa a yankin Arewa maso yamma a jihar Sakkwato.
Za mu iya cewar a cikin mutanan da suke neman kujerar Shugaban kasa Atiku Abubakar ne mutum na farko da ya fara kaddamar da yakin neman zabensa, kuma tuni har ya sake tsallakawa yankin Arewa ta tsakiya inda ya kuma kaddamarwa a can.
Wannan shi ne ke nuna babu takunkumin fara yakin neman zaben mukamin Shugaban kasa a yanzu, da kuma kujerun majalisun dokoki na tarayya. A irin wannan lokaci na zabe na Iya cewar lokaci ne nai wuyar sha’ani, Domin kuwa yanzu kusan lokaci ne da ake neman jama’a ta kowace hanya, Yan Siya sa da masu takara na amfani da matasa maza da mata domin nuna yawan magoya bayansu.
Matasa da zauna gari banza na samun dama a wannan lokaci inda ake debo su mota mota ana yawo da su guraren taruka ba dan komai ba sai don ayi amfani da su, a nuna yawan mabiya. Wasu da dama daga wannan lokacin ba zaka sake ganinsu ba, daga an zabe su sun koma Abuja Sai ka ga kamar anyi Ruwa an dauke.
Za ka sha mamaki ka ga dan majalisar da aka zaba ko a matsayin sanata ko wakili ya tafi Abuja ya tare da iyalansa, bai taba zuwa yaji halin da al’ummarsa suke ciki ba Sai yanzu da aka sake buga gangar Siya sa sannan ya dawo yana tara mutane a gidansa yana dafa abinci yana basu yana basu ganye da makamai da Yan kudade.
Sai ka ga irin wadannan takadaran ‘Yan Siya sa sune wadanda wasu masu tsukakken tunani suke gani a matsayin gwaraza, bayan a can majalisar masa ba abin da suke yi sai wakiltar kansu basa kawo wani Abu da zai taimaki al’ummarsu Sai su da iyalansu, a gida kuma an manta da su, babu su babu labarinsu Sai kuma yanzu suka dawo ana musu kallon gwaraza.
Wannan ba karamin abin kunya bane, ace an dauki irin wadannan mutane a matsayin masu kishin al’umma ko kishin kabila. Suna can sun tara dukiya nai dumbin yawa su da iyalansu, sun kuma dawo sun kakabawa mutane ‘Yan takarkaru a matakai daban daban ana musu kullon su din jagorori ne duk abin da suke so shi za a aiwatar.
Su kuma mabiya daman an jahiltar da tunaninsu ba za su gane irin illa da ake musu sun dauka hakan wani abin ado ne. Akinmu shi ne Mu fadakar kuma Mu Ankarar da mutane musamman matasa akan yadda ake amfani da su ana samun biyan bukata su kuma an barsu ko oho.
Matasa ya dace a shiga taitayi a san cewar lallai yanzu kan mage ya waye. Ba yadda za ace a wannan karni na ashirin da daya Ace matasa suna kara kifewa tare da maida kansu baya da yin gurguntacce tunani kan makomarsu da ta iyalansu shekaru masu zuwa.
A yanzu muna lokaci na wayewa tare da sanin ya kamata. Bai kamata Mu bari wasu ‘Yan kwaya bugaggu su maida mu tamkar gayaunarsu ba, ba muda wani amfani Sai dai a bamu dan abin da bai taka kara ya kairya ba Mu kuma muna ya ihun Sai wane ko garin ba Kowa, alhali wannan wanen bai amfana mana komai ba balle yankinmu da al’umma da yake cikinta.
Irin wadannan miyagun mutane ba abin da suke Sai sayawa kansu da iyalansu maka makan gidaje da motoci na alfarma suna mana kallon jahilai bamu san me muke ba. Mu kuma saboda talaucin zuci da gaggawa Mu dinga ganin kamar su me za su yi mana arziki ba Allah ba.
Shi ya sa ka ga mutane suna yiwa dan Siya sa fadanci da bambadanci sannan su koma suna yiwa ‘ya ‘yansa fadanci da bambdanci. Kamar taskar azikin duniya a hanunsu take ana ganin kamar sune za su yi wa mutane arziki, alhali kuwa da bazar mutane suke rawa suna tarawa kansu dukiya da arziki, sun kai yaransu kasashen Turai sun yi karatu amma nan sun bar mana makarantu da asibitoci tamkar ragowar Yaki.
Idan ka shiga asibitocinmu musamman na kauyuka Sai ka ga dauka yaki akai aka Gama a gine ginen asibitin, haka makarantunma suke, babu malamai bahu kujeru babu kyakkyawan yanayin koyo da koyarwa.
A irin wannan yanayi yaran talakawa da ake amfani da su ana gwada yawan jama’a suke karatu a makarantun gwamnati, sannan aka lalata asibitocin da za a kai yaransu Idan ba su da lafiya. Daman kuma tuni aka sace kudaden kananan hukumomi inda nan ne inda suka fi kusa da mutane a gwamnatance.
Gwamna ya shekara takwas yana kashe kudaden kananan hukumomi yana zuwa ba a aljihunsa ya mayar da Kowa bawansa Sai abin da yake so shi za ai ko da kuwa mutane basa so. Shi yana ganin tunda yana da damar iko akansu Sai abin da ya ga dama zai shukawa mutane kuma dole su karba.
Lokaci yayi da za mu nunawa irin wadannan ‘Yan Siya sa basu Isa ba, a nuna musu cewar mutane ba kayan gadonsu bane, su fahimci cewar shiru shiru ba tsoro bane, kuma mutane su nuna lallai sun san ‘yancinsu ta hanyar zabar mutane masu kirki wadanda ba za su dadi dukiyoyinsu ba su tarawa iyalansu. Kar mutane su yi la’akari da jam’iyya indai mutumin arziki ya fito ko a ina yake a zabe shi.

Exit mobile version