Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home MAKALAR YAU

Yayin Da Ake Shirin Fara Allurar Riga-Kafin Korona A Nijeriya

by Muhammad
January 10, 2021
in MAKALAR YAU
3 min read
Rigakafin Korona
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Nijeriya ta shiga sahun kasashen duniya a tafarkin yaki da a bazuwar annobar korona, ta hanyar kokarin gudanar da allurar riga-kafin kamuwa da cutar mai saurin yaduwa. An dade ana kai ruwa- rana tsakanin manyan kasashen duniya kan batun aiwatar da riga-kafin mai cike da sarkakiya, al’amarin da wasu kasashe ke dari-darin aiwatar da shi.

Sakamakon hakan manyan kasashen duniya sun yi ittifaki wajen daukar matakin bai-daya na yaki da annobar tare da bazama wajen nemo riga-kafin cutar. Al’amarin da ya tilasta wa kasashe yan ku-ci-ku-bamu karbar tsarin hannu-biyu. Kamar yadda aka saba, wasu da dama sun bayyana shakku dangane da allurar riga-kafin annobar, kamar yadda ya faru da ta shan-inna a kasar nan.

samndaads

Wani binciken mu ya gano yadda wasu yan Nijeriya suka yi wa riga-kafin gurguwar fahimta tare da shan alwashin kin amincewa da yunkurin. Kuma ta yuwu wannan yana da alaka da zargin siyasantar da sha’anin annobar kana da zarge-zargen da wasu ke danganta cutar koronan dasu na rashin tabbas tare da yadda wasu mahukunta ke wasa da hankulan talaka dangane da annobar.

A hannu guda kuma, a tashin farko yan Nijeriya da dama sun dauki batun korona bil hakki tare da kaffa-kaffa da bazuwar cutar wanda daga baya wasu al’amurra su ka yi canja tunanin yadda ake kallon lamarin musamman yadda aka sha bayar da alkaluman masu dauke da cutar sabanin abinda mutane ke gani a zahiri tare da ware makudan kudade da sunan yaki da ita fiye da abinda yafi ci ma yan kasa tuwo a kwarya; matsalar tsaro, cutar maleriya da sauran su, wadanda ke halaka rayuka amma ba a dauke su da cikakken muhimmanci ba.

Bugu da kari kuma, hukumar yaki da gagararrun cutuka masu saurin yaduwa ta kasa (NCDC) ta sanar da cewa za a fara allurar riga-kafin annobar ga ma’aikatan jinya hadi da jami’an tsaron shige da fice, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya (WHO) tare da NAFDAC su ka tsara.

Haka kuma, hukumar ta tsara cewa za a yi wa kaso 40 cikin dari na yan Nijeriya riga-kafin; kimanin mutum miliyan 80 kafin karshen wannan shekara tare da karin wani kaso 30 cikin dari; daidai da mutum miliyan 60 a shekarar 2022 mai zuwa, wanda ya doshi kaso 70 cikin dari na adadin yan kasar kenan (kimanin mutum miliyan 140) zuwa watan Disamba.

Wani hanzari ba gudu ba, lura da yawan yan Nijeriya sama da miliyan 200 ta kawo wannan adadi na allurar, sabanin Afrika ta Kudu ta kawo 750,000 domin yi wa mutum miliyan 1.5.

Haka zalika kuma, kila irin wannan jita-jitar ce tayi tasiri a kunnen gwamnatin Nijeriya wanda wasu rahotanni sun nuna cewa za a fara riga-kafin ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo tare da sauran manyan mukarraban gwamnati a matakin farko.

Wanda jin cewa riga-kafin zai fara ta kan shugaban kasa da mataimakin sa, su ma gwamnonin jihohin kasar sun bayyana anniyar yin riga-kafin kai tsaye ta kafafen yada labarai don jama’a su gani da idonsu.

Shugaban kungiyar gwamnonin ne ya sanar da hakan, Dr Kayode Fayemi, ranar Jummu’a a birnin tarayya Abuja a sa’ilin da yake amsa tambayoyin yan jaridu, bayan ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa.

“Za mu yi hakan ne domin nuna wa yan kasa fa’idar allurar riga-kafin tare da bayar da tabbacin cewa tana aiki sosai.”

Masu hikimar magana sun ce: babu rami me ya kawo zancen sa. Sannan wasu yan Nijeriya su na cewa: ta ya za a yi kura da shan duka gardi da karbar kudi!

A nashi bangare, Daraktan kula da allurar riga-kafin cutuka masu saurin yaduwa a hukumar kiwon lafiya matakin farko ta kasa (NPHCDA), Dr. Bassey Okposen, ya bayyana cewa wannan adadi na allurar riga-kafin annobar korona 100, 000 daga kamfanin BioNTech-Pfizer zai shigo Nijeriya kafin karshen wannan wata.

Abin zuba ido a gani, shin ko yan Nijeriya za su maimata halayyar da suka nuna a lokacin takwaransa na shan-inna ko za su bayar da cikakken hadin kai? Wanda lokaci ne kawai zai nuna hakan.

SendShareTweetShare
Previous Post

Matasan ‘Yan Jarida Sun Karrama Hajiya Maryam, Jagabar Matan Zazzau

Next Post

Yadda Za Ka Hada Lambar Wayarka Da NIN Dinka

RelatedPosts

APC

Canjin APC Ko Canjin Rigar Mahaukata?

by Sulaiman Ibrahim
3 days ago
0

Abubuwa sun bi sun damalmale, komai ya rincabe, kayan masarufi...

Shekarar

Shekara Kwana: Bankwana Da Shekarar 2020 (3)

by Muhammad
4 days ago
0

Wani mahimmin batu da ya kamata ace an yi bitarsa...

Shugaba Sam

Bankwanata Da Shugaba Sam

by Muhammad
5 days ago
0

Abdulrazaq Yahuza Jere, Da farko kafin in bayyana bankwanata da...

Next Post
NIN

Yadda Za Ka Hada Lambar Wayarka Da NIN Dinka

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version