Yayin Da Majalisa Ta Sake Fasalin Dokar Bankuna Da Cibiyoyin Kudi…

Bankuna a Nijeriya, sun fara tsayuwa da kafafuwansu ne tun a karshen shekarar 1980 zuwa farko-farkon shekarar 1990, ta hanyar dokar da ta ba su damar cin gashin kansu, ba tare da wata tsangwama ba, a karkashin mulkin Soja. Babu shakka, wannan doka ta matukar jawo hankalin ‘yan kasuwa wajen sanya kudadensu a Bankuna.

Kazalika, domin magance matsalolin da ke tasowa a daidai wannan lokaci tare da kokarin ceto Bankunan daga fadawa wani mummunan hali, Sojoji sun bijiro da doka a shekarar 1991, wadda za ta baiwa Bankuna da sauran Cibiyoyin Kudi kariya. Haka aka yi ta gyaran wannan doka lokaci zuwa bayan lokaci har bayan zuwan demokradiyya, inda ‘Yan Majalisa suka dora daga inda aka tsaya.

Ko shakka babu, wannan doka ta bayar da muhimmiyar dama wajen ci-gaban harkokin Bankuna a Nijeriya tsawon lokuta. Haka zalika, sauran Cibiyoyin harkokin kudi da Kimiyya da Fasaha na bukatar ire-iren wannan kulawa, domin kara inganta su.

Don haka, wannan Kamfanin Jarida ya lura da cewa, tsawon lokaci ana samun bunkasa tare da ci-gaba a fannonin harkokin kudi, samar da sabbin Cibiyoyin kula da su daban-daban da kuma amfani da su ta hanyoyin da suka dace. Saboda haka, wadannan ci-gaba da aka samu sun tilasta bukatar samar da dokokin kula da Bankuna tare da sanya musu idanu a Nijeriya.

Wannan bukata ce ta sanya muka nemi Majalisar Dattawan Nijeriya, wanda tuni Sanata Uba Sani da Betty Apiafi suka gabatar da kudirin a gaban Majalisa, sannan an yi masa karatu na farko da na biyu tare da mika shi kacokan zuwa babban Kwamati mai kula da harkokin Bankuna, Inshorar Kudi da kuma sauran Cibiyoyin Kudi domin tattaunawa a kai.

A bangaren nasu na Majalisa, tattaunawar ta jawo mahawara akan wasu masu ruwa da tsaki, wadanda suka turo da tasu matsayar kan wannan tinga-tinga. Cikin wadanda suka gabatar da nasu jawabin, akwai Babban Bankin Nijeriya (CBN).

A jawabin Babban Bankin, ya nemi Kwamatin ya yi la’akari tare da kara wasu bangarori, wadanda za su karawa sake fasalin dokokin Bankuna da Cibiyoyin Kudi (BOFIA 2020) kima. A yayin da yake gabatar da wannan din, Babban Bankin ya yi nuni tare da kawo muhimman misalai dangane da kwarewa da kuma ilmin da yake da ya samu shekara da shekaru ta hanyar daidaitawa da kula da Bankuna da sauran Cibiyoyin Kudi a Nijeriya.

Cikin shawarwarin da Bankin CBN ya bayar, ya hada da bangarori goma sha daya, wanda yake so Majalisar Dattawa ta hada da shi a cikin dokar. Da farko, ya nemi Sanatocin su sake yin nazari wajen farfado da Bankunan yadda za su yi kunnen doki da sauran na kasashen duniya a bangaren ci-gaba. Haka zalika, Babban Bankin Kasar na bukatar sake tantance nasa aikin da kuma na Hukumar NDIC na kasa.

Har ila yau a namu ganin, yana da matukar muhimmanci a kawar tare da tantance ayyukan da ka iya tasowa, musamman a daidai lokacin da Hukumar NDIC ta nemi da cewa, lallai ita ce ke d a hurumi ko ikon samawa Bankuna lasisi. Haka nan, a gefe guda kuma Bankin CBN na ikrarin cewa, shi ne yake da wannan hurumi, don haka ya kyautu a cikinsu a fidda guda daya wanda zai rika kula da wannan bangare na Bankuna.

Don haka, a cikin wannan kudiri na Bankin CBN ya bayyana karara cewa, samun dokokin da za su baiwa Bankuna kariya, za su taimaka wajen bunkasa harkokin Masana’antu da sauran Cibiyoyin harkokin kudi tare da samun daidaito a cikinsu.

Mun fahimci cewa, sabbin shiga wannan harka ko kuma wadanda suka shigo harkokin Banki daga baya-bayan nan, musamman wadanda ba sa ta’ammali da kudin ruwa, Abokan huddodinsu ko kasuwanci na jin dadin harkoki da su ta fuskoki daban-daban. Sannan kuma Babban Bankin Nijeriya, na ci-gaba da yunkurin ganin an tabbatar da su a matsayin masu gudanar da harkokin kasuwanci na-daban.

Kazalika, Bankin CBN ya ci-gaba da kalubalantar hanyoyin biyan kudi tare da daidaita samar da ayyukan ci-gaba a Bankuna, wadanda su ne kashin bayan aikin Bankunan kacokan. Don haka, kamar yadda masu iya magana ke cewa, “mai daki shi ya san inda yake yi masa yoyo”, a namu ra’ayin muna ganin cewa, Babban Bankin Nijeriya na son a bijiro da dokar da tattare dukkannin wasu ci-gaba da Bankuna za su iya samu a nan gaba, domin amfanin kawunansu. Sannan mun yi matukar farin ciki, ganin yadda Sanatoci suka dauki wannan al’amari da muhimmanci tare da yin dogon nazari a wannan bangare na Bankuna, wanda ake fatan duk sa’ilin da ya zama doka kowa zai yi farin ciki da shi.

Exit mobile version