Rundunar Sojin Kasa Ta kasa Nijeriya Ta Nada Birgediya Mohammed Yerima a Matsayin sabon mai magana da yawunta.
Sanarwar ta futo ne a yau Talata daga bangaren Hulda da Jama’a na Rundunar, cewa Birgediya Yerima shi ne ya maye gurbin Birgediya Sagir Musa wanda aka sauya wa wurin aiki.
Sanarwar ta ce kafin sabon mukaminsa, Birgediya Yerima shi ne Mataimakin Darakta mai kula da Ajiya na Hedikwatar Tsaro. Ya kuma taba zama Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar.
Gwamna Ortom Ya Yabawa Umarnin Buhari Na Hana Mallakar AK47 Ba Bisa Ka’ida Ba
Daga Rabiu Ali Indabawa, Gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom a ranar...