Connect with us

WA'AZIN KIRISTA

“Yesu Shi Ne Hanya”

Published

on

Wurin Karatu – Yohanna 14:6

Kan Magana: “Yesu ya che masa Ni ne hanya Ni ne gaskiya, Ni ne rai: ba – mai zuwa wurin uban sai ta wurina (Yohanna 14:6)

To! Baban Magana wai mahaukachi ya hau kura! Wannan ayar ta tono babban magana day a yakamata mu yi kya kyawar nazari akan ta. In ana magana hanya to ana nufi ne da ina ne da mutum zai bi zuwa wani wuri. Sai gashi yesu Almasihu na tabbatar wa duniya da cewa shine wannan hanyar.

Watau in Yesu na cewa shine hanya, to wanne irin hanya ne shi? Bisa ga koyaswar littafin maitsarki, muna sane da cewa Yesu ya zo duniya domin ya chichi masu zunubi ko kuwa, domin ya chichi duniya daga zunubansu. Allah ya ceiko shi chikin duniya domin duka wadanda suka bada gaskiya a gareshi bas zasu taba lalace ba amma zasu sami rain a har abada.

Ashe, da yesu na cewa shine hanya, manufarsa shine hanyar cheto ga kowane Bil Adama mai bada gaskiya a gareshi. Yesu ya cigaba da cewa a chikin wannan ayar da cewa shine “gaskiya”. Watau matuka yesu ya tabbatar mana da cewa shine gaskiya to yakamata san da cewa cheto bata samuwa sai an san gaskiya. Masu iya magana sun ce; “Daga kin gaskiya sai bata” Da gaskiya ne ake samun cheto, domin yesu Almasihu ya tabbatar da cewa.

“Ku a san gaskiya kuma, gaskiya kwa za ta yantadda ku” (Yohanna 8:32). In sanin gaskiya kan kai ga samun yantaswa, to ashe Yesu Almasihu shine maicheto. Ma’ana duk wanda ya san gaskiya ashe ya san Yesu Almasihu kuma san Yesu sanin cheto.

Wannan ayar na kunshe da abubuwa masu mahimanchi dangane da matsayin shin Yesu Almasihu da ikonsa na cheton Bil Adama. Wannan aya na tabbatar mana da cewa, Yesu Almasihu shine hanya watau hanyan cheto ga kowani irin mutun da ya bada gaskiya a gareshi.

Yesu Almasihu ya kara tabattar mana da cewa shine gaskiya watau gaskiyan da kowane irin mutum ke bukata domin samun cheto Ubangiji Allah.

Sai a Karshe Yesu Almasihu ya kara tabbatar mana da matsayin sa kuma ikonsa a kan cheto da cewa “Ni ne rai.” A takaice Yesu Almasihu shine hanyan zuwa ga samun cheto, shine gaskiyar da ake samu cheto a karshe y ace shine wannan raid a ake bida. A Yohanna 3:16 Yesu Almasihu ya tabbatar mana da cewa shine rain a har abada. Watau in mun hada Yohanna 8:32, Yohanna 14:6 da Yohanna 3:!6 zamu yarda cewa Yesu Almasihu shine “hanya, gaskiya da kuma rai – kama yadda littafin Maisarki na cewa: “Yesu y ache masa, Ni ne hanya, Ni ne gaskiya, Ni ne rai: ba mai zuwa wurin uban sai ta wurina” (Yohanna 14:6)

Wannan tabbacin cheto ne ga kowane irin mutumin daya bada gaskiya ga mutuwa da tashiwan Yesu Almasihu. Anan, Yesu Almasihu ya nuna mana da cewa shine wuka shine nama game da magana cheto. Ina so mu gane da abinda Yesu Almasihu ke nufi da cewa shine hanya, shine gaskiya da kuma shine rai babu mai zuwa wurin Allah uba sai tawurinsa.

Watau saduwa da Allah ubangiji shine cheto, amma wanna bata samuwa sai mai bukatan cheto ya sami hanyar cheto, watau Yesu Almasihu. Duk mutumin da ked a bukatar cheto to, wajibi ne maibukatar ya san gaskiya domin, sanin gaskiya shine  zai kawo yantaswa. Da samun hanyan cheto da gaskiya da ke kawo cheto shine ke kai kowane mutum zuwa ga samun rain a har abada.

Doles ne mutuna da Yesu Almasihu ya ce mana a Yohanna 3:16 da cewa duk wanda ya bada gaskiya gareshi ba zai sami raina har abada. Daga Tsohon Alkawari zuwa sabon Alkawari Allah Ubangiji ya bada annabcen – annabcen annabawa sun tabbatar da cewa Yesu Almasihu shine hanya zuwa ga cheto. Domin wadanan annabce annabcen sun chika akan Yesu Almasihu a matsayi shine hanyan cheto, shine gaskiya da ke kawo cheto da kuma shine raid a kowa ke bida.

Mutuwan Yesu Almasihu a kan giciye da kuma tashiwan sa daga matattu  shine tabaccin cheto ga wadanda suka bada gaskiya a gareshi. A chikin littafin ishaya 53, Allah Ubangiji ya bayana mana wahalan da Yesu Almasihu zai sha domin cheton Bil Adama. Babu wanda ya iya chikar wannan annabcin a dukan annabawa sai dai Yesu Almasihu.

Yesu Almasihu ya bada ran sa domin cheton BIl Adama, shine ya tabbatar da gaskiyan maganar littafin maitsarki watau Yohanna 14:6. A wannan ayan, Yesu Almasihu bai gajiya ba, sai daya tabbatar mana cewa shine hanyar cheto, gaskiyan da ke kawo cheto da kuma rain a har abada Yohanna 3:!6.

Babu annabi ko manzon Allah guda, day a taba yin kira a kan cewa shine hanyan cheto, ko shine gaskiya zuwa ga cheto ko kuma shine dallilin samun rai na har abada a’a sai dai Yesu Almasihu kadai. Babu annabi ko manzo guda ya taba yin kira da cewa duk wanda ya bada gaskiya gareshi ba zai taba lalacewa ba amma zai sami rai ne har abada, sai dai Yesu Almasihu kadai.

A karshe Yesu Almasihu ya kara tabbatar mana wata abu da babu ko annabi da manzo guda daya taba yi wata kira akan cewa: “Yesu ya che mata, Ni ne tashin matuttu, Ni ne rai: Wanda ya bada gaskiya gareni ko ya mutu za shi rayu” (Yohanna 11:25)

Wadanan hujjoji sun isa mu yarda da cewa Yesu Almasihu shine hanya, shine gaskiya da kuma rai, watau shine maicheton duniya.

Shalom! Shalom!! Shalom!!!
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: