Daga Mohammed Chinade, Yobe
Shugaban kungiyar hadakar ‘yan kasuwa na karamar hukumar Potiskum a jihar Yobe Alhaji Isa sakatare ya yi kira ga gwamnatin tarayya da kuma daidaikun kungiyoyin bada tallafi na cikin gida da na waje da su hanzarta wajen cika alkawuran da suka dauka na bada tallafin tun kafinal’umma su dawo daga rakiyarsu.
Shugaban ya bayyan hakan ne ga wakilinmu a ofishinsa da ke garin Potiskum dongane da yadda aka sa mambobinsu ke ta cika takardu daniyyar za a basu tallafi da kuma rance amma har yanzu shiru kamar an shuka dusa,
Alhaji Isa sakatare ya ci gaba da cewar, daga shekarar 2015 zuwa wannan shekara ta 2017 an sa sun cika fom na neman rance dakuma neman tallafi sama da 7 daga bankunan bada rance mai sauki ga ‘yan kasuwa da kuma kungiyoyin bada tallafi kan abin da ya shafiyankunan da suka yi fama da rikicin Boko-Haram na cikin gida da na waje amma har yau babu koda guda da aka ba su.
Daga nan sai shugaban kungiyar ‘yan kasuwar ya nemi jama’a da su ci gaba da bada goyon baya ga wannan gwamnati ta shugaban kasaMuhammadu Buhari dongane da muhimman