Daga Abubakar Abba, Kaduna
Sakamakon kiraye-kirayen da ake yi wa Shugaba Muhammadu Buhari na ya sake tsayawa takara a zaben kasa ta shekarar 2019, wani Soja mai ritaya, Manjo Mohammed Bashir Shu’aibu Galma, ya shawarci Buharin da ya yi koyi da marigayi tsohon shugaban kasar Afirka ta kudu Nelson Mandela na kin fito wa takarar.
Galma, ya bada shawarar ce a wata ganawa da ya yi da manema labarai a Kaduna.
Ya ce, ganin cewar Shugaba Buhari Dattijo ne, kuma ya taba rike mukamin shugaban kasa a karshin mulkin soja gashi kuma yanzu ya zama shugaban kasa karkashin mulkin farar hula, kin tsayawarsa takara a shekarar 2019 zai kara masa kima a idon duniya, kamar yadda marigayi Mandela ya yi na kin fito wa takara a kasar shi.
Galma wanda yana daya daga cikin mambobin Cibiyar Buhari ta kasa, ya ci gaba da cewa, Shugaba Buhari kusan duk ya cika alkawuran da ya daukar wa ‘yan Nijeriya lokacin yakin neman zabe, “kamata ya yi ya nuna dattaku ya ki fitowa kamar yadda wasu ‘yan kasa suke ta kiraye-kiraye na ya sake tsayawa takara.
Ya yi misali da cewar, shugaba Buhari ya yi alkawarin samar da tsaro da yakar cin hanci da rashawa da ya zamo rowan dare a kasar nan kuma ya samu cin nasara, ya yi alkawarin dai-daita tattalin arzikin kasa kuma ya cika, inda hakan ya janyo masa yabo har daga kasashen ketare.
Galma, ya kuma shawarci shugaban da ya yi tankade da rairaya a cikin ministocinsa, inda ya ce musamman ministocin da ba su taka wata rawar gani ba wajen gudanar da ayyukan ma’aikatunsu, ko kuma ya rage wa masu nauyin da ya dora musu ta hanyar raba ma’aikatunsu.