Likitoci sun yi nasarar yi wa dan wasan da Barcelona ta saya mafi tsada a bana, Ousmane Dembele aiki a ranar Talata.
Dakta Sakari Oraba ne ya jagoranci aikin a wani asibiti a birnin Helsinki da ke Finland, kuma likitan Barcelona Dakta Ricard Pruma ke kula da dan kwallon.
Dan wasan mai shekara 20 dan kwallon tawagar kasar Faransa ya koma Spaniya da taka-leda daga Borussia Dortmund a cikin watan Agusta.
Dembele ya yi rauni ne a wasan da Barcelona ta ci Getafe 2-1 a gasar La Liga wasan mako na hudu a ranar Asabar.
Kungiyar ce ta sanar da cewar dan kwallon zai yi jinyar wata uku da rabi zuwa hudu.
Kungiyar ta Barcelona dai ta buga wasa na biyar a gasar ta laliga inda tayi raga-raga da kungiyar Eiber daci 6-1 wasan da dan wasa Messi ya zura kwallaye hudu sai Luis Suarez yaci daya yayinda shima sabon dan wasa Poulinho dan kasar Brazil.