Yi Wa ‘Yan Siyasa Da Dalibai Gwajin Kwayoyi Ya Zama Dole –NDLEA 

Takarkaru

Hukumar NDLEA ta sake jaddada bukatar yi wa daliban jami’a da ‘yan siyasa gwajin kwayoyi. Hukumar ta dage cewa, akwai bukatar ‘yan Nijeriya su ba da amanar baitul malinsu ga masu hankali. Haka zalika, gwajin zai shafi bangarori da dama na cudanyar aiki da siyasa a fadin Nijeriya in ji hukumar. Shugaban Hukumar hana Sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ne ya bayyana bukatar ‘yan siyasa da ke neman ofisoshin gwamnati da daliban manyan makarantu a yi musu gwaji na tabbatar da basa shan kwayoyi.

A cewar wata sanarwa daga Daraktan yada labarai na hukumar, Femi Babafemi, shugaban NDLEA din ya yi magana ne a ranar Talata a Abuja yayin da yake gabatar da takarda kan ‘Shaye-shayen miyagun kwayoyi da tsaron kasa: Samar da mafita’, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito. Sanarwar ta nakalto Marwa na jaddada bukatar ‘yan siyasa su yi gwajin shan kwayoyi yayin da zabe ke karatowa a wasu jihohi da kuma fadin kasar.

“Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Marwa (mai ritaya) ya sake jaddada bukatar ‘yan siyasa masu neman ofis din gwamnati da daliban da ke neman shiga manyan makarantu su yi gwajin kubuta daga miyagun kwayoyi” in ji sanarwar.

Ya ce akwai bukatar mutane su ba da amanar gudanar da baitul malinsu da jin dadinsu a hannun ‘yan siyasa masu hankali. Ya bayar da hujjar cewa babu wani mai rike da mukamin gwamnati da ke cikin maye da zai iya yin tunanin ci gaba. Marwa ya ce irin wannan lamari ya shafi daliban da ke neman shiga manyan makarantu a fadin kasar.

Ya ce saboda hujja mai karfi da ke tsakanin shaye-shayen miyagun kwayoyi da kalubalen tsaro a duk fadin kasar, dole ne a hada karfi da karfe don shawo kan matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi kai tsaye. Ya ce, “Game da wannan, muna yin iya kokarinmu a bangarenmu na hukumar NDLEA.

Akwai canjin yanayi a tsarinmu na fuskantar abubuwan maye. A baya cikin watan Janairu, Marwa ya ce zai gabatar wa da gwamnati bukatar gwajin shan kwayoyi ga dukkan manyan makarantun gaba da sakandare, kamar yadda The Guardian ta ruwaito. Ya kara da cewa za a kuma gudanar da gwajin ne ga mambobin bautar kasa (NYSC), sabbin ma’aikata, dukkan hukumomin tsaro, sabbin daukar ma’aikata, da kuma gwajin ba zata ga wadanda gwamnati ta nada mukamai.

Exit mobile version