Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Ƙaramar hukumar Tarauni ta Kano ta sami nasarar yiwa yaran yankin sama da 70,000 rigakafin ciwan shan-Inna. Shugaban sashen kula da lafiya a matakin farko na ƙaramar hukumar, Kwamred Nura Haruna Rimin Gado ya bayyana hakan bayan kammala ƙarƙare zagayen rigakafin na wannan karon.
Ya ce, tun kafin soma rigakafin a Tarauni anyi tarurruka na horaswa da fadakarwa da masu ruwa da tsaki kan aikin rigakafin da kuma de kuma masu ruwa da tsaki na yankin da suka hada da dagatai,masu unguwanni da malamai da hakimi dan tabbatar da nasarar rigakafin.
Kwamred Nura Haruna Rimin Gado ya yaba wa irin namijin ƙoƙarin da Jami’in riƙo na ƙaramar hukumar Tarauni Alhaji Auwalu Musa Madaci Rano ya yi wajen samar da duk kayyakin da ake rabawa ga yara da iyaye mata dan jawo hankalinsu zuwa karɓar rigakafin da suka hada da sabulai,da alawowi da abin busa na yara.
Shi ma ɗan majalisar jaha mai wakiltar yankin.Alhaji Habu ya bayarda irin wanan tallafi na magungunan zazzabin sauro.
Kwamred Nura Haruna Rimin Gado ya ce, a wannan karon ba,a samu wasu mutane da yawa da suka tirjewa karɓar rigakafin ba, sakamakon wayar da kan al’umma da aka riƙayi akai-akai tasa mutane na gane muhimmancin yin rigakafin ga lafiyar yaransu.
Nura yayi kira ga iyaye su cigaba da baiwa wannan shirin hadin kai da goyon baya,nan gaba kadan za,a gudanarda rigakafin ciwan kyanda da sauran cutuka da shima yakamata iyaye su bada haɗin-kai da goyon baya da samun nasarar aiwatarwa.