Abubakar Abba" />

Yin Aiki Da Tsofaffin Dokoki Ya Zamo Wa Cibiyar Kula Da Lafiyar Dabbobi Kalubale

Cibiyar kula da lafiyar dabbobi ta kasa BCN ta bayyana cewa, karancin kudi da kayan da aka dai na amfani da su da kuma tsofaffin dokoki ne manyan kalubalen da suka sa Cibiyar ta gaza cimma muradun da suka kafa Cibiyar.

Cibiyar ta sanar da hakan ne a cikin wata takardar bayan taro da ta fitar bayan kammala wani taron bita da ta shirya wa ‘yanta a babban birnin tarayyar Abuja.

A cewar Cibiyar, rashin wanzar da gudanar da mulki na gari da kayan aiki  ya na daya daga cikin kalubalen da Cibiyar ta ke fuskanta.

Sanarwar ta kara da cewa,  akwai kuma rashin hada karfi da karfe a tsakanin kwararrun kungiyoyi a fannin kula da lafiyar dabbobi, inda hakan ya ke kara janyo rashin samar da wadatattun dabbobi a kasar nan.

Sanarwar ta kara da cewa, rashin mayar da hankali kan shirin ilimantar da masu kiwon dabbobi a kasar nan sama da shekaru da suka gabata, hanakn ya sanya Cibiyar ta gaza cimma burinta da sa a gaba.

Ta kara da cewa, rashin samar da tsarin gudanar da mulki ingantacce, hakan na shafar Kwalejin da ake yi wa dabbobi tiyata.

Sanarwar ta kara da cewa, rashin samar da kyakywan tsari da kuma rashin yin hadaka, hakan na kara zamowa kalubale ga Cibiyar, musamman ga kasashen da su ke  a cikin kungiyar ECOWAS, inda ya kara da cewa, Cibiyar ta kuma yanke shawarar hada Cibiyar hada Cibiyar da na’ura ta zamani.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, za ta yi iya kokarinta wajen ganin an samubta tsaffin dokokin yadda za su da ce da na zamani, inda ta kara da cewa, za ta kuma tashi kai tsaye wajen ganin an kara samar da kudade a cikin kasafin kudi da ake ware wa Cibiyar da kuma kara samar wad a Cibiyar kudaden shiga ta hanyar masu ba ta gudaunmawa da kuma sauran kungiyoyin da ke a kasashen waje.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, za ta yi dukkan mai yuwa wajen ganin ta cika mafarkinta na kafa asibitin dabbobi na musamman a babban birnin tarayyar Abuja.

Ta kuma bayyana cewa, za ta iya kokarinta wajenm ganin an kara samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar nan, tare da samar da kyakyawan yanayi.

A wani labarin kuwa, Kamfanin kimiyyar kere-kmkere na Noma dake Nijeriya, ya ba da shawarar yin amfani da fasaha don rage matsalar annobar Korona  kan fannin aikin  noma a kasar nan.

OFAB a cikin wata sanarwa da babbar jami’a a kamfanin  Dakta Rose Gidado ta fitar ta  ce, za a iya magance kalubalen samar da abinci da rarrabawa yayin barkewar annobar ta hanyar yin amfani da fasaha.

Sanarwar ta kara da cewa: rashin yiwuwar rayuwar manoma na Afirka wanda ya zama kusan kashi 65 a cikin dari,  na yawan mazaunan za a iya gwada su a lokacin da kuma bayan barkewar cutar ko yaya dai, ra’ayinmu ne cewa sabbin hanyoyin fasaha na iya ba da gudummawa ga gudanar da wannan cutar tare da rage tasirin tasirinta akan aikin noma.

A cikin kula da cutar, kisa mai kisan gilla ta Korona, ta ta’allaka ne kan binciken kimiyya da sabbin abubuwa ciki har da ilimin kimiyyar kere-kere wanda zai iya isar da magani nan bada jimawa ba.

Bugu da kari, za a iya magance kalubale a fannin samar da abinci da rarraba wa yayin barkewar cututtukan ta hanyar fasahar kuma a  halin yanzu, Afirka na iya samun damar ci gaba da fasaha ta zamani don magance kalubalen noma fiye da kowane lokaci na tarihi.

A cewar sanarwa, wasu daga cikin wadannan kimiyoyin sun hada da nau’ikan amfanin gona mai bada amfanin gona wanda zai iya yin aiki sosai a cikin yanayin fari, zai iya tsayayya da kwari da cututtuka kuma su na iya amfani da abubuwan gina jiki sosa, inda sanarwar ta kara da cewa, sauran fasahohin sun hada da zabin sarrafa gona da kuma hanyoyin aikin gona na dijital don sarrafa amfanin gona da watsa ilimi.

 

Exit mobile version