Cutar koda, cuta ce da ke da matukar hatsari ga Bil-Adama kuma a yanzu haka wannan cuta rahotannin masana na nuna cewar Jihar Yobe ce ke kan gaba a dukan fadin tarayyar kasar nan da ke da yawan jama’ar da ke dauke da wannan cuta ta koda. A kan hakan ne wakilinmu MUHAMMAD SANI CHINADE ya samu tattaunawa da Kwamishinan ma’aikatar lafiya a Jihar Yobe, Dakta MUHAMMAD BELLO KAWUWA wanda ya gaskata wannan rohoton da masana da ke cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya (FMC) da ke garin Nguru a Jihar suka bayar a kwanakin baya kan cewar, Jihar Yobe ce ke kan gaba a dukan fadin kasar nan da yawan mutane da ke dauke da cutar koda (kidney) tare da kawo irin matakan da suke shirin dauka don magance ta. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
’Yallabai, me za ka ce dangane da wani rahoto da wasu masana kan harkokin kiwom lafiya cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya (FMC) dake Nguru suka bayar kan cewar, Jihar ne ke kan gaba a yawan mutanen da ke dauke da cutar koda (kidney) a fadin kasar nan?
Alal hakika wannan rahoto da ya fito daga masana a asibitin Nguru dangane da wannan cuta ta koda tabbas haka ne domin a halin da ake ciki wannan cuta ta koda cuta ce da ke shirin zama
alakakai ga al’umma kasancewar a kullum bazuwa take yi kamar wutar daji ta inda ake samun yawaitar masu kamuwa da ita.
Bangaren Jihar da aka fi samun yawaitar masu kamuwa da wannan cuta dai shine bangaren arewacin Jihar ta Yobe wanda shine aka fi samun yawaitar masu kamuwa da wannan cuta ta koda babu kakkautawa musamman ma a kananan hukumomin Geidam, Bade, akusko,Yusufari,karasuwa, Nguru da Machina.
Daga lokacin da kuka samun wannan rahoto ya zuwa yanzu ko akwai wani hobbasa da kuka yi dangane da hakan?
A hakikannin gaskiya tun ma kafin wannan rahoto gwamnatin Jihar Yobe ta farga cewar, lalle wannan matsala ta cutar koda ta kunno kai a Jihar sai aka fara daukar mataki, to amma kuma fitowar wannan rahoto na masana mai nuna Jihar Yobe ne ke kan gaba a masu dauke da wannan cuta sai hakan ya sa muka shiga bincike ba dare ba rana don gano masu dauke da wannan cuta don kai musu daukin gaggawaganin cewar jinya ce dake da tsadar dawainiyarta da kuma hanyoyin da za a bi don shawo kanta to alhamdulillah.
Kamar yaya?
A halin da ake ciki gwamnatin Jihar ta yunkura ta wajen gano masu dauke da wannan cuta tun tunin tare da daukar dawainiyar wasu daga cikinsu da cutar tafi tsamari inda ake kai su kasashen
ketare don yi musu magani yayin da wadanda kuma cutar bata yi tsamari ba ake daukar dawainiyar wanke musu odar da yi musu magani a cibiyar kiwon lafiya FMC dake Nguru ko wasu asibitocin dabam.
Bayan haka kuma tunin gwamnan Jihar Alh Ibrahim Geidam ya bada umarnin kafa kwakkwaran kwamitin masana kan harkokin kiwon lafiya da zai faraaiki a sabuwar shekara mai kamawa ta 2016 In Allah ya so don gano abubuwan dake haifar da yawaitar kamuwa da wannan cuta da kuma binciken irin ruwan da suke sha da gwada kasar yankunan da abin yafi kamari da sauran dabaru don taka wa lamarin birki.
Yallabai me zai hana gwamnatin Yobe ta samar da wata cibiya ta musamman don kula da masu dauke da wannan cuta ta koda?
A yanzu haka da nake magana cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya (FMC) da ke Nguru na da wata cibiya ta musamman da ke kula da masu dauke da cutar wadda gwamnatin Yobe da hannun ta cikin kafuwar wannan cibiya ta Nguru don haka ashe ka ga muna da cibiya da ke kula da wannan cuta ta oda, kuma anan Damaturu ma In Allah yaso za mu yi kokarin samar da sashin da zai kula da masu dauke da wannan cuta a babban asibitin tunawa da marigayi Sani Abaca da ke Damaturu.
Ko gwammatin Yobe ta nemi wasu kungiyoyin bada tallafi kan harkokin kiwon lafiya na kasa da kasa da na cikin gida dangane da wannan cuta?
A gaskiya ba mu yi haka ba amma kuma shi taimako babu wanda ba ya so, don haka matukar in mun samu wani wanda ke sha’awar taimaka wa bangaren ciwon oda ya nuna son taimakawa muna maraba da hakan.