Muhammad Maitela" />

Yobe Ta Aiwatar Da Kashi 94.92 Na Kasafin Kudin 2020- Hon. Bego

Hon. Bego

Kwamishina a ma’aikatar yada lanarai, al’adu da harkokin yau da kullum a jihar Yobe, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kokari wajen aiwatar da kaso 94.92 cikin dari na kasafin kudin 2020, wajen inganta rayuwar al’umnar jihar.

Malam Abdullahi Bego, ya bayyana hakan ranar Alhamis inda ya ce gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni ta aiwatar da ayyuka na kimanin naira biliyan 87.3 daga cikin jimlar naira biliyan 91.9 na jimlar kasafin 2020, wanda ya yi daidai da kaso 94.92 cikin dari na ayyukan da ta gudanar a jihar.

Hon. Bego, ya bayyana hakan a taron manema labarai da ya gudanar a birnin Damaturu, inda ya kada baki ya ce, “Gwamnatin jihar Yobe a karkashin Gwamna Mai Mala Buni ta yi hobbasar aiwatar da muhimman ayyukan bunkasa ci gaban al’ummar jihar wanda ya shafi ingantattun manufofin habaka tattalin arziki.”

Ya kara da cewa gwamnati ta yi kokari wajen aiwatar da kasafin da ta ware wa harkokin yau da kullum, wanda ya doshi sama da naira biliyan 26.1 wanda ya yi daidai da kaso 99.08 cikin dari zuwa ranar 24 ga Disamban 2020. Sannan da aiwatar da manyan ayyuka da makamantan su wanda ya doshi naira biliyan 36.5, kimanin kaso 91.43 da biliyan 24.6 daidai da kaso 96.07 cikin dari a wannan fannin.

Baya ga wannan kuma, kwamishinan ya lissafta wasu daga cikin manyan nasarorin da gwamnatin Buni ta samu na aiwatar da kasafin, wadanda su ka kunshi ginin kasuwanin zamani a manyan garuruwan jihar na Damaturu, Potiskum, Gashua, Nguru, kana da sake farfado da kamfanonin jihar- kamfanin fulawa, na leda, na kwanon rufi hadi da na takin zamani a cikin shekarar 2020.

Har wala yau kuma da karin wasu ayyukan ginin sabuwar hanya mai tazarar kilomita 40 daga Gujiba zuwa Mutai, gina tagwan hanya mai tazarar kilomita 25.5 wadda ta tashi daga Damaturu zuwa Kalalawa, hanyar Nguru zuwa Balanguwa mai nisan kilomita 16, da hanyar Damagum zuwa Gubana, kana daga Abbatoir zuwa Potiskum da sauran su.

Malam Bego ya ce gwamnatin jihar Yobe ta gina rukunan ajujuwan karatu 12 wadanda su ka kunshi ajujuwa 62, dakunan ba-haya 24 tare da ofisoshi 18 a makarantu daban-daban a jihar, sannan da daukar nauyin karatun dalibai 273 wajen karanta fannin shari’a tare kari wasu zuwa kasashen waje.

Dadin dadawa, kwamishinan ya bayyana cewa a cikin 2020 gwamnatin Mai Mala Buni tayi nasarar gina dakin kwanan dalibai mai cin gadaje 200 a makarantar koyon aikin jinya da unguwan-zoma a jihar (Shehu Sule College of Nursing and Midwifery) da ke birnin Damaturu tare da sayo kekunan daukar majinyata 39 a shekarar kudin.

A hannu guda kuma, Alhaji Abdullahi Bego ya ce gwamnatin jihar ta kashe sama da naira miliyan 200 tsuffin ma’aikata kudin fansho na wata-wata, tare da kashe naira miliyan 200 wajen biyan daliban jihar kudaden tallafin karatu, kana da ware naira miliyan 114 domin sayo kayan tallafa wa matasan da aka koya wa sana’o’in dogaro da kai a jihar.

 

 

Exit mobile version