Yobe Za Ta Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomi Ranar 27 Ga Fabarairu

Yobe

Hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Yobe ta bayyana aniyar gudanar da zaben kananan hukumomin jihar 17 tare da kansilolin su ranar 27 ga watan Fabarairun 2021 mai zuwa.

Shugaban hukumar, Dr Mamman Mohammed, shi ne ya sanar da hakan a taron manema labarai, a ofishin hukumar da ke Damaturu, ranar Talata. Ya ce sama da mutum 1,365, 000 ne za su kada kuri’u a zaben shugabanin kananan hukumomi 17 da kansiloli 178 a fadin jihar.

Bugu da kari kuma, shugaban hukumar ya nemi hadin kan baki dayan jami’an tsaro a jihar wajen samun nasarar zaben, wanda hukumar ta ce jam’iyyu 16 ne za su fafata.

“Saboda kokarin da muke yi shi ne, mu na bukatar inagantaccen yanayin da zai bamu damar gudanar da zabe mai cike da yanci, gaskiya da limana ba tare da wani tangarda ba,” in ji shi.

Har wala yau, shugaban hukumar zaben ya bayyana daukar matakan sauya wasu rumfunan zabe zuwa waau gurare ko hade wasu waje daya saboda yanayin matsalar tsaro a wasu sassan jihar Yobe.

A hannu guda kuma ya nemi kafafen yada labarai a jihar su taimaka wajen wayar da kan jama’a dangane da tsare-tsaren hukumar wanda hakan zai taimaka jama’a su fito ranar zaben.

Dr Mohammed ya yi kira na musamman ga jami’an hukumar da masu ruwa da tsaki a aikin gudanar da zaben kan cewa kar su tsoma baki a lokacin zaben.

“Na kama sunan ku ne kebance saboda muhimmiyar gudumawar da kuke da a gudanar da wannan zaben,” a ta bakin Dr Mohammed.

 

Exit mobile version