Daga Muhammad Maitela, Damaturu
Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Gaidam ya bayyana cewar gwamnatin sa ta ja damarar farfado da ayyukan noman rani ta hanyar amfani da shiri na musamman na noman rani domin alkinta filayen noma da Allah ya azurta yankin dasu dake shimfide a yankunan kananan hukumomin Nguru da Gaidam, wajen bunkasa tattalin arzikin jihar a fannin noma shinkafa da alkama, tare da shan alwashin cewa nan gaba kadan jihar Yobe zata kasance a sahun gaba a sha’anin.
Gwamnan yayi wannan furucin ne a sa’ilin da ya kai ziyarar aiki a filayen noman rani wanda gwamnatin jihar ta ware a wadannan yankunan a tsakiyar makon da ya gabata, yayin da ya bayyana matukar gamsuwar sa dangane da yadda aikin ke gudana tare da shan alwashin cewa gwamantin sa zata bada himma wajen dorewar wannan shirin noma na alkama, masara, shinkafa da sauran kayan albarkatun gona. Inda ya tabbatar da cewa nan gaba kadan kwalliya zata biya kudin sabulu.
Alhaji Ibrahim Gaidam ya bayyana cewa “bisa abinda idona ya gani a wadannan kadada da muka kebe domin noman rani ya karfafa gwiwa ta kuma nan gaba kadan zamu kasance a sahun gaba wajen samar da shinkafa da alkama. Zamu yi duk kokarin mu wajen baiwa wannan shirin kwarin gwiwa dangane da abinda duk yake bukata ta hanyar fadada filin da kayan aiki ga manoman mu domin su kasance zaratan manoma da zasu rinka safarar kayan su daga nan zuwa wasu wurare”.
Gambomi Goni ya sake nanata cewa, aikin dasa iraruwa zai kama gadan- gadan ne a yankin Nguru cikin watan October, kuma manoma 1, 000 zuwa 1, 200 zasu ci gajiyar wannan shirin.
Har wala yau ya ce“kuma zamu kasa watanin shekara zuwa gida uku ne; daga October zuwa Maris zamu saka alkama, shinkafa kuma mu shuka ta tsakanin Maris zuwa Yuli, sannan muyi amfani da tsakanin Yuli zuwa Satumba wajen shuka masara. Kuma muna kyautata zaton girbe ton hudu zuwa biya a kowacce kadada”. Inji shi.Har wala yau ya ce“kuma zamu kasa watanin shekara zuwa gida uku ne; daga October zuwa Maris zamu saka alkama, shinkafa kuma mu shuka ta tsakanin Maris zuwa Yuli, sannan muyi amfani da tsakanin Yuli zuwa Satumba wajen shuka masara. Kuma muna kyautata zaton girbe ton hudu zuwa biya a kowacce kadada”. Inji shi.Har wala yau ya ce“kuma zamu kasa watanin shekara zuwa gida uku ne; daga October zuwa Maris zamu saka alkama, shinkafa kuma mu shuka ta tsakanin Maris zuwa Yuli, sannan muyi amfani da tsakanin Yuli zuwa Satumba wajen shuka masara. Kuma muna kyautata zaton girbe ton hudu zuwa biya a kowacce kadada”. Inji shi.