Khalid Idris Doya" />

Yuguda Ya Barnatar Da Biliyan 200 Na Bauchi, A Cewar Kwamiti

Kwamitin da ke da alhakin bibiya da tabbatar da dawo wa al’umman Bauchi da dukiyoyinsu da aka handame, ya zargi tsohon gwamnan jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda da barnatar da zunzurutun kudi da ya yawansa ya kai biliyan dari biyu (N200bn) a lokacin da yake gwamnan jihar.

Kwamitin ta ce wannan kason, yana daga cikin magudan kudade   matsayin ‘Ecological Fund’ daga shekarar watan Mayun 2007 zuwa watan Mayun 2015 lokacin da Yugudan ke gwamna.

Gwamnan Bauchi, Bala Muhammad dai ya kaddamar da kwamitin ne a ranar 12 ga watan Yuli da daura musu alhakin bibiya da bankadowa hadi da tabbatar da kwato kwabo da sisin jihar da wasu suka yi wadaka da su a lokacin da suke bakunan aikinsu.

Masu magana da yawun kwamitin, Umar Barau Ningi  da Malam Musa Azare sun shaida hakan a wani taron manema labaru da suka kira a Bauchi, kwamitin ya bayyana cewar ya dauki matsayar yin aiki da hukumomin da abun ya shafa domin tabbatar da sun samu nasara kan aiyukan da suka sanya a gaba.

Ningi ya ce, kwamitin ya amshi korafe-korafe guda 279, ba ya ga wadannan, kwamitin ya kuma samu bayanai game da kason gwamnatin tarayya, rancen gida da na kasashen waje, kudaden tallafi, da sauran kudaden da suka shigo na tallafi wadanda suka fadada bincike daga karamin mataki zuwa babba a kansu.

Umar Barau Ningi ya ce, “Kamar yadda muka binciko daga ofishin babban Akanta Janar na kasa, adadin kudi naira N393,867,570,547.75 ne jihar Bauchi ta amso a matsayin kasonta daga watan Mayun 2007 zuwa Mayun 2015.

“Sannan kuma, kwamitin ya samu nasarar gano N386,500,736,402.86 daga bayanan asusun ajiya na gwamnatin jhar Bauchi.

“Kudin da yawansu ya kai biliyan N564,851,151,690.05 ne Bauchi ta samu daga watan Mayun 2007 zuwa Mayun 2015, sama da naira biliyan N200,000,000,000.00 daga cikin wannan kason, kwamitinmu ya gano gwamnatin Isah Yuguda kawai ta ballagazar da su da barnatarwa ba tare da yi wa jama’an jihar aiyukan a zo a gani da su ba,” A cewar kwamitin.

Kwamitin ya jero hanyoyi daban-daban da aka samu kudade a jihar a karkashin gwamnatin Isa Yuguda da kuma wadanda ta gamsu da an kashesu a bisa hanyoyin da suka dace da kuma maguden biliyoyin da kwamitin ta yi zargin gwamnatin Yuguda da lalatawa.

Kwamitin dai ya sha alwashin yin duk mai iyuwa wajen kwato wa jama’an jihar Bauchi hakkokinsu da ake zargin wasu da handamewa.

Exit mobile version