Yunkurin Amurka Na Takaita Ci Gaban Sin Ta Hanyar Fakewa Da Batun Xinjiang Ba Zai Yi Nasara Ba

Daga CRI Hausa

Kakakin ofishin kasar Sin a MDD, ya bayyana rashin gamsu tare da adawa mai karfi ga wani taro na gefe da Amurka da Birtaniya da Jamus da wasu tsirarun kungiyoyi masu zaman kansu za su gudanar kan yanayin hakkin dan Adam a jihar Xinjiang ta kasar Sin.

Kakakin ya bukaci wadanda suka dauki nauyin shirya taron da su soke gudanar da shi, domin zai yi katsalandan cikin harkokin gidan kasar Sin, yana mai kira da mambobin MDD su ma su yi watsi da shi.

Kasashen 3 da sauran masu daukar nauyin taron wadanda ke adawa da kasar Sin, na amfani da batutuwan hakkin dan Adam a matsayin wata dabara ta siyasa, a yunkurin haifar da rabuwar kawuna da tashin hankali a Xinjiang, tare da tsoma baki cikin harkokin gidan Sin, da kuma kawo tsaiko ga zaman lafiyar kasar.

Yanayin da ake ciki a Xinjiang yanzu, shi ne mafi kyau da aka samu a tarihi, inda aka samu zaman lafiya da saurin ci gaban tattalin arziki da jituwa tsakanin al’ummomin mabanbantan kabilu.

Amurka da sauran kawayenta sun yi nisa a yunkurinsu na shirga karairayi da amfani da batutuwan da suka shafi Xinjiang wajen dakile ci gaban Sin da hargitsa kasar. A cewar kakakin, dukkan kabilun jihar Xinjiang na adawa da wannan manufa, cikinsu har da al’ummar Uygur da daukacin Sinawa, sannan kuma ba za ta taba yin nasara ba. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CRI Hausa)

Exit mobile version