Khalid Idris Doya">

Yunkurin Kyautata Tattalin Arziki Ne A Gabanmu, Inji Gwamnatin Gombe

Gwamnatin jihar Gombe ta bayyana cewa tana da babban burin nausawa da bunkasa tattalin arzikin jihar gaba, ta hanyar gina al’umma da samar da tattalin arziki mai kwarin yin gogayya ta ko wace fuskar.
Mataimakin gwamnan jihar Dakta Manassah Daniel Jatau ne ya bayyana hakan ranar Juma’ar yayin da ya wakilci Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a wurin taron bita na shekara ta 2021 da aka shiryawa shugabannin kamfanin bunkasa fasahar sadarwa na Gwamnatin tarayya Galady Backbone wadda ya gudana a hotel din kasa da kasa dake jihar Gombe.
Gwamnan ya ce “Nan ba da jimawa ba za mu kaddamar da shirin ci gaba na shekaru 10 daga 2021 zuwa 2030, wanda zai daura jihar kan turbar cimma muradun ci gabanta na matsakaici da dogon zango.”
Ya kara da cewa jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba kan kokarin ta kawo ci gaban tattalin arziki da bunkasa rayuwar jama’a ta ko wace fuska.
Da ya ke yabawa kamfanin fasahar sadarwan na G. Backbone bisa shirya taron bitan, Dakta Manassah Jatau ya ce bada horo ya kan kimtsa ma’aikata da shugabanni sosai don samun cimma muradu da burorin kowane kamfani ko ma’aikata.
A na shi jawabin, ministan sadarwa da raya tattalin arzikin zamani Dr Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bukaci shugabannin kamfanin bunkasa sadarwan Gwamnatin na Galady Backbone su fi maida hankali kan sabin tunani da kirkire-kirkire, da tsara buri mai dogon zango da kuma maida hankali kan kyautatawa da biyan bukatun abokan hulda.
Ya ce, “Ta haka ne kawai kamfanoni ke wanzuwa, su bunkasa har ma su daure tsawon shekaru aru-aru.”
Isa Ali Pantami ya ce cikin shekara guda, Gwamnatin Tarayya ta magance kaso 90 cikin dari na matsalolin dake addabar kamfanin na G. Backbone don maida Nijeriya kasa mai ci gaban fasahar sadarwa dama tabbatar da cin gajiyar dimbin damammakin da sashin ke tattare da su.

Exit mobile version