Yunkurin Masu Ruwa Da Tsaki A Nahiyar Afirka Wajen Samar Da Takin Zamani
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yunkurin Masu Ruwa Da Tsaki A Nahiyar Afirka Wajen Samar Da Takin Zamani

byAbubakar Abba
2 years ago
Takin Zamani

Daya daga cikin abinda ke ciwa fannin aikin noma Tuwo a Kwarya a nahiyar Afirka shine karancin takin zamani.

Sai dai, domin a lalubo da mafita kan wannan kalubalen, wasu hukumomi sun dukufa kan yadda za su manoma a nahiyar sun samar wa da manoma takin, musamman kan farashi mai sauki.

  • An Jefar Da Jariri Dan Kwana 2 A Sansanin ‘Yan Gundun Hijira A Edo
  • Sudan: Jami’o’in Nijeriya Sun Sha Alwashin Bai Wa Daliban Da Aka Kwaso Guraben Karatu

Misali, hukumar samar da abinci da kuma bunkasa aikin noma da ke a karkashin majalisar dinkin duniya FAO da kuma shirin samar da abinci da ke a  karkashin majalisar WFP sun yi hasashen cewa, za a samu karancin abinci saboda tarnakin da fannin na samar da abinci ke fuskanta.

Bugu da kari, don a magance irin wannan kalubalen, masu ruwa da tsaki a fadin duniya a fannin aikin noma sun gudanar da taro, inda suka yi nuni da cewa, akwai matukar bukatar a yi amfani da kayan aikin noma na zamani, musamman don a tabbatar kananan manoma sun samu takin zamani kuma kan lokaci don a samar da abinci, musamman mai gina jiki ga alumma.

Wasu daga cikin tattaunawar da aka yi irin wannan tarukan, sun nuna yadda wasu yankunan da ke a nahiyar Afirka ke kan yin kokari wajen samar da wadatacen takin zamani da ilimantar da manoman kan sanin ingantacciyar kasar noma da za su yi shuka akai da yadda za su zuba takin zamani da sauransu.

Har ila yau masu bayar da dauki a fannin aikin noma sun zuba dala biliyan 30,musamman don a bunkasa yin noma a nahiyar Afirka ke na sama da shekaru hudu  masu zuwa.

Baya ga wannan, mahalarta taron sun kuma yi kira da a gaggauta samar da takin zamani ga manoman da ke a nahiyar kuma a cikin farashi mai sauki.

A cewar kungiyar masana’antun sarrafa takin zamani ta kasa da kasa, a nahiyar Afirka IFA, ana yin amfani da buhun takin zamani mai nauyin kilo 12 a kowacce kadadar noma daya.

Hakazalika, Cibiyar bincike kan tsare -tsaren abinci ta kasa da kasa IFPRI ta bayyana cewa, takin zamani da moma ke yin amfani da shi a Nijeriya da Kenya da kuma wasu sassan a Afrika ako wacca kadadar yin noma, ya kai kasa da kilo 50 idan aka yi la’akari da yadda ake yin amfani da shi Malaysiya, inda ake yin amfani da akalla kilo 1,570 ako wacce kadadar noma daya sai kuma a kasar Hong Kong, inda ake yin amfani da kilo 1,297 ako wacce kadadar noma daya, inda kuma a kasar Bangladesh ake yin amfani da akalla kilo 278 ako wacce kadadar noma daya.

Bugu da kari, Cibiyoyi ta IFPRI ita ma ta goyi bayan taron musamman don tattauna wa kan yadda za a samar wa da manoma da ke a nahiyar  takin zamani da kuma samar wa masu safarar takin kudade  don a shigo da sanadaran da ake sarrafa takin zamanin.

Hakazalika, kulab din da ke samar wa da manoma takin zamani wato Afrikom, shi ma ya gudanar da wata ganawa a Accra, babban birinin kasar Ghana kan yadda za a samar wa da manoma takin zamani.

Kulab din ya gudanar da ganawar ce wadda ta kasance a karon farko bisa hadaka da Cibiyar habaka takin zamani ta kasa da kasa IFDC tare da kuma kungiyar samar da takin zamani a  yammacin Afrika WAFA.

Sun yi hakan ne bisa kokarin yadda za a samar wa da manoma takin zamani a Afrika da kuma irin sauye -sauyen da aka samu a fannin na samar da takin zamani a Afrika.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

October 3, 2025
Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo
Noma Da Kiwo

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

October 3, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi

September 27, 2025
Next Post
An Fara Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa Da Na ‘Yan Majalisa A Turkiyya

An Fara Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa Da Na 'Yan Majalisa A Turkiyya

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version