CRI Hausa" />

Yunkurin Pompeo Na Kawo Illa Ga Dangantakar Sin Da Afirka Ba Zai Cimma Nasara Ba

akataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo, ya yi bayani a kwanakin baya, inda ya zargi kasar Sin da yin amfani da aikin yaki da cutar COVID-19, wajen bada rancen kudi ga nahiyar Afirka, ta yadda za ta tarawa kasashen nahiyar basussuka. Pompeo ya ci gaba da yada jita-jita da zargin kasar Sin, a wani mataki na yunkurin kawo illa ga dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka, matakin da kuma ko alama ba zai cimma nasara ba.

Sin da Afirka, sun dade suna sada zumunta tsakaninsu, da kiyaye samun bunkasuwa. Bayan bazuwar cutar COVID-19, Sin da Afirka sun nuna goyon baya ga juna, da yin hadin gwiwa wajen yaki da cutar. A yayin da kasar Sin ta fuskanci yanayin bazuwar cutar COVID-19 mai tsanani, dukkan ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar AU sun sanar a watan Febrairu cewa, suna tsayawa gwamnatin kasar Sin, da jama’arta wajen yaki da cutar. Bayan da aka samu bazuwar cutar COVID-19 a nahiyar Afirka, kasar Sin ta samar da kayayyakin yaki da cutar da dama ga kasashen Afirka cikin hanzari, da kuma tura tawagogin masu aikin jinya da masanan yaki da cutar.
A gun taron kolin musamman na hadin gwiwar yaki da cutar COVID-19 da aka gudanar tsakanin Sin da Afirka a watan Yunin da ya gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da soke basusukan da Sin ta baiwa wasu kasashen Afirka ba tare da kudin ruwa ba, bisa tsarin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, wadanda wa’adinsu zai kare a karshen shekarar 2020. Kana Sin ta yi alkawari cewa, bayan da aka cimma nasarar nazarin allurar rigakafin cutar COVID-19 da fara amfani da su, da farko za a samar da su ga kasashen Afirka.
Ba ma kawai kasar Sin na maida hankali ga aikin yaki da cutar COVID-19 ba ne, har ma ta taimakawa kasashen Afirka wajen farfado da tattalin arzikinsu a wannan lokaci. Kasashen Afirka su ma sun nuna yabo ga alkawarin da Sin ta yi musu, da kuma ayyukan da Sin ta gudanar.
A halin yanzu, kasashen Afirka suna fuskantar kalubale da dama, don haka ya kamata kasashen da abin ya shafa, su kara gudanar da ayyukan taimakawa kasashen Afirka, wajen yaki da cutar COVID-19, da samun bunkasuwa da sauransu. Kuma bai kamata a yada jita-jita, ko kawo cikas ga sauran kasashe da suke kokarin taimakawa Afirka ba. Kasa da kasa ciki har da kasashen Afirka, sun san wane ne yake taimakawa kasashen Afirka, kuma wane ne ke siyasantar da aikin yaki da cutar COVID-19.
A kwanakin baya bayan nan, an fi samun yaduwar cutar COVID-19 a kasar Amurka, inda yanayin yaki da cutar ya tsananta. A matsayin muhimmin jami’in gwamnati mai ci ta kasar Amurka, Pompeo ya kyale yanayin yaki da cutar a kasarsa, inda ya mayar da hankali gaba daya wajen zargin kasar Sin, da kuma kokarin hadin gwiwar yaki da cutar a tsakanin kasa da kasa.
Duk wani yunkurin kawo illa ga dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka domin siyasa ba zai samu nasara ba. An yi kashedi ga Pompeo, da wasu ’yan siyasar kasar Amurka, da su dakatar da zargin sauran kasashe dake yin kokarin yaki da cutar COVID-19. Maimakon haka kamata ya yi su maida hankali kan aikin yaki da cutar a kasar Amurka.
Har ila yau, ya kamata su maida aikin ceton rayukan jama’a a gaban komai, da kara gudanar da ayyukan taimakawa juna, wajen inganta hadin gwiwar kasa da kasa kan yaki da cutar. (Zainab Zhang)

Exit mobile version