Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Yunkurin Ta da Rikici A Hong Kong Ba Zai Yi Nasara Ba

Published

on

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo, ya fada a jiya Litinin cewa, yayin da kasar Sin ke kafawa, da aiwatar da dokar tsaron kasa mai alaka da yankin Hong Kong na kasar, kasar Amurka za ta dakatar da sayar da kayayyakin tsaro ga yankin Hong Kong, kana za ta kayyade samar da fasahohi masu alaka da tsaron kasa, da amfanin jama’a ga yankin Hong Kong, daidai da yadda take kayyade fasahohin da take fitarwa zuwa babban yankin kasar Sin.
Ko da yake mista Pompeo ya kan yi ikirarin cewa, yana zama tare da jama’ar Hong Kong, amma a wannan karo ya nuna halayyarsa ta gaskiya, inda yake neman hana yankin Hong Kong samun ci gaba, gami da haifar da matsala ga kasar Sin. Sai dai, yunkurin ‘yan siyasan Amurka na ta da rikici a yankin Hong Kong, sam ba zai yi nasara ba.
Bayan aukuwar cece-kuce game da shirin gyaran wata doka a yankin Hong Kong a watan Yunin bara, wasu gungun mutane na kasashen waje, sun yi ta kokarin rura wuta a yankin, inda suka ingiza aikace-aikacen nuna karfin tuwo da ta’addanci, ta yadda za su kara tsananta a titunan Hong Kong, lamarin da ya zamo barazana ga zaman rayuwar jama’ar yanki, da tsaron kasar Sin.
Don daidaita wannan matsala, ya zama dole a yi kokarin samar da wata ingantacciyar doka mai karfi. Idan mun yi nazari kan tsarin dokoki na kasar Amurka, za mu ga akwai dumbin dokoki masu alaka da tsaron kasa. Sai dai a wannan karo, suna ta cece kuce game da mataki mai dacewa da kasar Sin ta dauka. Hakan ya nuna niyyar kasar Amurka na ta da rikici a Hong Kong, da hana kasar Sin ci gaba.
To sai dai kuma takunkumin da kasar Amurka ke neman kakabawa yankin Hong Kong, zai haifar da matsala ga ita kan ta, saboda da kasar Amurka tana samun rarar ciniki da ta kai dala biliyan 30 daga yankin Hong Kong a kowace shekara. Sa’an nan, kayayyakin da batun takunkumin ya shafa, yankin Hong Kong zai iya shigo da su ta sauran hanyoyi, don haka, takunkumin ba zai yi illa sosai ga Hong Kong ba.
A sa’i daya kuma, yadda aka kafa, da fara aiwatar da dokar tsaron kasa mai nasaba da yankin Hong Kong, zai samar da damar yanke hukunci ga baragurbin dake neman ta da rikici a yankin, lamarin da nan gaba zai tabbatar da ci gaba mai dorewa a yankin. (Bello Wang)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: