Daga Abubakar Abba
Manoma a yankunan da ake yawan samun hare hare-haren ‘yan bindiga da yin garkuwa da mutane, ba su iya zuwa gonakansu domin nomawa inda suka bayyana cewa wannan babbar matsala ce da take nuna alamar tunkarowar yunwa.
An ruwaito cewa, ganin iirin yadda rashin tsaron ya janyo a wasu jihohin, manoma da dama, na ganin za a samu karancin abinci a jihohin, idan har ba a magance matsalar ba.
Masali, a makonnin da suka wuce, jami’an tsaro sun samu nasarar kakkabe masu aikata nugayen ayyuka, kamar na ‘yan ta’addar Boko Haram a yankin Arewa Maso Gabas tare da ragargazar wasu ‘yan bindiga da masu garkuwa a wasu sassan na Arewa Maso Gabas da yankin Arewa ta Tsakiya.
Sai dai, duk da wannan nasarar da jami’an suka samu, har yanzu akwai tsoro cikin zaukantan wasu manoman, tare da kara jin tsoron rashin kankamar daminar bana a jihohinsu.
A jihar Katsina, kauyawa da dama, sun arce daga matsagunansu saboda haren-haren ‘yan bindiga, musamman kamar yadda wasu mazauna a yankin Sheme da ke Karamar Hukumarukumar Faskari wasu manoman suka bayyana cewa, ko da yake ba za su iya sanin adadin yawan kauywan da suka arce daga kauyukansu ba, inda suka ce, amma adadin, ya kusan 100, musamman ganin cewa, ‘yan bindigar, tuni suka mayar da kauyukan a matsayin mafakarsu.
A yankin Ruwan Godiya kadai, akwai kauyuka kamar su, Shawu, Unguwar Goga, Yantuwaru, Gidan Dogo, Unguwar Nadaji, Hayin Najafa, Unguwar Baidu, Kanawa, Hitaru da kuma Unguwar Haji.
Akasarin wadannan gurarare, a yanzu, ‘yan bindiga sun mayar da su mafakarsu, inda kuma ‘yan bindigar ba su mamaye ba, manoman da ke a kauyukan ba sa iya zuwa gonakinsu saboda tsoron kada a sace su.
A yankin ‘Yar Malamai manoma ba sa iya zuwa gonakinsu da ke a kauyuka kamar su Mununu, Zari, Kuka Shida, Dogon Fako, Kibai, Bakarya, Liggel, Zarin Dudu da Zarin Kwari, saboda tsoron kar a kashe su.
Har ila yau, a Jihar Yobe wasu manoman sun shafe sama da shekara shida, haka a kauyukan da ke a Karamar Hukumar Gujba, daya daga cikin yankin da ‘yan ta’addar ayyukan Boko Haram ya yi kamari, manoma a yankin, tuni suka yi watsi da gonakinsu.
A watan Janairu, yankin ya fuskanci matsin daga hare-haren ‘yan ta’adda har kusan sau shida, inda hakan ya janyo salwatar rayuka da dama wasu kuma suka samu munanan raunuka, lalata dukiyoyi, makarantu, kone gidaje, gonaki da wasu dakunan shan magani.
A Jihar Zamfara, manoma da dama na ci gaba da fuskantar kalubalen zuwa gonakinsu domin noma su, wasu kuma tuni suka yi watsi da gonakinsu saboda tabarbarewar al’amaran tsaro.
Shekaru da dama, an sace wasu mazauna a kauyukan da dama, musamman manoma, inda bayan sun biya kudin fansa, aka sako su.
A jihohin Kebbi da Neja nan ma haka lamarin yake, sai dai, ragargazar da jami’an soji suka yi wa ‘yan bindiga da sauran masu aikata muggan ayyuka, matsalar ta dan ragu, amma har yanzu, manoman na ci gaba da fuskantar kalubalen zuwa gonakinsu domin yin noma.
Dagacin Zuru John Mani ya bayyana cewa, ‘yan bindiga da suka fito daga Jihar Zamfara da Neja, sun mamaye wasu yankuna a Karamar Hukumar Sakaba da ke a Jihar Kebbi, tare da fasa Ruagage suka sace Shanu sama da 100, sai dai dai babu wanda ya rasa ransa a yayin farmakin na su.
Bugu da kari, kimanin gidaje 16,000 har na manoma ‘yan bindiga suka tarwatsa a Zuru a cikin watanni shida da suka gabata. An kuma ruwaito cewa, sama da manoma 20,000 daga cikin yankin Kashi 50, ba za su iya yin noma a kakakar noma ta bana ba, hakan ya sa yunwa ta fara tunkaro jihar, musamman ganin cewa akasarin al’ummar jihar manoma ne.
A Borno kuwa, akasarin mazuna karkara manoma ne, sai dai, saboda tabarbarewar rashin tsaro manoma da dama sun yi watsi da gonakansu shekaru da dama da suka gabata.