Daga Musa Mohammed Rimi, Kaduna
Wata ƙungiya mai yaƙi da yunwa tsakanin ƙananan yara a jihar Kaduna mai suna ‘The Kaduna Emergency Nutrition Action Plan (KADENAP)’ ta bayyana cewar kimanin yara 120 ne suka rasu, a sanadiyyar rashin cin abinci mai gina jiki a cikin shekara ɗaya kacal a jihar.
Shugabar wannan ƙungiya, matar Gwamnan jihar ce, Hajiya Aisha Ummi El-rufai ta bayyana haka a wani taron manema labarai da ta kira a Kaduna a makon nan.
A ta bakinta, an ƙaddamar da wannan ƙungiya da take Shugabanci ne a farkon wannan shekarar, bayan samun rahotanni masu sosa rai a akan yara, masu fama da tamuwa a sanadiyyar ƙarancin abinci mai gina jiki.
Ta ce, alƙaluma sun nuna yara 11,540 aka kai waɗannan cibiyoyi daga watan Janairu zuwa Agusta.
Daga nan Hajiya Ummi ta alaƙanta talauci, jahilici, rashin zuwa asibiti ga mai juna biyu, da kuma rashin abinci mai gina jiki.