Gwamna Uba Sani na jam’iyyar APC ya kaddamar da gangamin yakin neman zaben jam’iyyar APC gabanin zaben Shugabannin kananan hukumomi da Kansiloli da ke tafe a jihar Kaduna a ranar 19 ga watan Oktoba.
Gwamna Sani ya mika tutoci ga ‘yan takarar shugabannin kananan hukumomi a karkashin jam’iyyar APC daga kananan hukumomi 23 da ke jihar.
- A Shirye Nake Na Rantse Da Alkur’ani Ban Saci Kudin Kaduna Ba – El-Rufai
- Murnar Ƴanci: Gwamna Fintiri Ya Yafe Wa Fursunoni Biyu
Da yake jawabi ga dimbin jama’a da suka halarci gangamin yakin neman zaben da za a yi a watan Oktoba, Gwamnan ya bayyana irin gagarumin ci gaban da gwamnatinsa ta samu a muhimman sassa a fadin jihar, musamman ta fuskar farfado da yankunan karkara da samar da ababen more rayuwa.
Gwamna Sani, ya bayyana cewa, tun bayan hawansa mulki, gwamnatinsa ta ba da fifiko wajen raya karkara, inda ta kaddamar da gina tituna 62 a fadin kananan hukumomi 23.
A bangaren Ilimi, gwamnatin ta gina makarantun sakandire 60. Bugu da kari, an rage adadin yaran da ba sa zuwa makaranta da 300,000 ta hanyar sabin tsarin ilimi da sabuwar gwamnatin ta kirkiro.
Gwamnan ya kuma bayyana nasarorin da aka samu a fannin kiwon lafiya, inda ya ce, an kammala inganta manyan cibiyoyin kula da lafiya 9, yayin da ake kan gina wasu sabbi 4, sannan kuma, an samar wa cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko 290 kayayyakin aiki.
Gwamnan ya jaddada cewa, kula da lafiya ba alfarma ba ce, hakki ne ga al’ummar jihar Kaduna.
Gwamna Sani ya yaba da shirye-shiryen rage radadin talauci wanda marasa galihu kimani mutum miliyan 1.9 suka amfana a karkashin gwamnatinsa a jihar.
A fagen siyasa, Gwamna Sani ya nuna jin dadinsa da yadda kimanin shugabanni 200,000 daga jam’iyyar adawa ta PDP suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, musamman a Kudancin Kaduna, wanda a cewarsa, wannan wata shaida ce ga ci gaban da gwamnatinsa ta samu wajen tabbatar da adalci, daidaito, da kuma bayyana gaskiya.
Da yake bayani kan yadda za a gudanar da zaben kananan hukumomi, gwamnan ya bayyana kwarin gwiwarsa ga ‘yan takarar jam’iyyar APC, inda ya ba su tabbacin cewa, za su samu cikakken goyon bayansa wajen ciyar da yankunan karkara gaba da kuma tabbatar da daidaiton tattalin arziki a fadin jihar.
Taron ya samu halartar wasu jagorori da shugabannin Jam’iyyar APC a jihar.
Daga cikin mahalarta taron, akwai Mataimakiyar Gwamna, Hajiya Hadiza Sabuwa Balarabe; da Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Dahiru Liman da sauran masu ruwa da tsaki ciki har da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Muktar Ramalan Yaro.
Talla