Masu hikimar magana sun ce ‘idan aski ya zo gaban goshi, ya fi zafi’. Wannan haka yake idan an danganta batun da siyasar Nijeriya kana da halayyar ‘yan siyasa waɗanda suka fara kai gwauro-mari a tsakanin al’umma, bayan dogon husufin da suka yi ba a jin ɗuriyar su. Da la’akari da zafafan kalaman jifar juna da yarfe. Hakan yana da nasaba da ƙaratowar kakar babban zaɓen 2019; duba ga yanzu an doshi cinye kaso biyu cikin ukun zangon shekaru huɗun zaben 2015.
Daga Muhammad Maitela, Damaturu
A daidai irin wannan lokaci ne ake sa ran dukkan ‘yan siyasa za su baje kolin su, mai cike da burin ɗarewa ɗoɗam kan kujerar madafun iko. Lokaci ne na fitar da maitar su a fili tare da ƙoƙarin naɗe hannun riga domin shiga fagen damben fasalta yadda za ta kaya a zawarcin jam’iyyu masu tagomashin magoya baya da ƙoƙarin jinjina nauyin kai gaci, ko akasin hakan. Yanayin da ke haifar da tankiyar da har sai an yi zaman sulhu a tsakanin ‘yan siyasar, al’amarin da ke kawo zaman ‘yan marina da rabuwa kowa da dutsi a hannun riga.
Bisa ga wannan ne, a cikin makonin da suka gabata hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa( INEC) ta fitar da jedawalin gudanar da babban zaɓen 2019; hukumar ta ayyana 16 ga watan Fabarairun shekarar a matsayin wadda a ciki za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa tare da na ‘yan majalisun tarayya. Sa’ilin da kuma zaɓen gwamnoni dana ‘yan majalisun dokokin jihohi zai wakana ranar biyu(2) ga watan Maris na shekarar.
Al’amarin da ya kai babu ga-maciji a tsakanin manyan jiga-jigan ta; tun daga matakin tarayya har zuwa jihohi. Halin da manazarta ke yi masa kallon tarnaƙi a lokacin gudanar da babban zaɓe na ƙasa mai zuwa. Duk da masu nazarin al’amurran siyasar Nijeriya sun yi bahasin cewa, sa’ar jam’iyyar PDP ɗaya ne; shi ne kan cewa jam’iyya ce wadda ta kafu da ƙafafun ta kuma wadda ta ke da manufa ƙwaya ɗaya. Saɓanin sabuwar jam’iyyar APC wadda ta kafu cikin mabambantan ra’ayoyin da manufofi.
Ɗaya daga cikin ruɗanin da ake zaton zai sake mayar da jam’iyyar PDP turken ta mai-caɓo shi ne na rikicin zaɓukan share- fage wanda kuma ya haifar da sa-in-sa da hararen juna a lokacin zaɓen 2015. Duk da kafin wannan, turka-turkar da kallon hadarin-kajin soma ne tun bayan rashin lafiyar shugaban ƙasa; marigayi Umar Musa Yar’aduwa, inda muhawara ta ɓarke dangane da ayyana Mista Jonathan matsayin muƙaddashin shugaban ƙasa, ƙarawa da ƙarau kuma, da bayan rasuwar sa; inda zaman doya da man-ja da kallon-kallo ya kunno kai a tsakanin ‘yan jam’iyyar PDP.
Ana sa ran cewa a wannan babban zaɓen mai zuwa na 2019 akwai yiwuwar samun gwabza-in-gwabza a tsakanin ƙusoshin jam’iyyar PDP; a fagen takarar kujerar shugabancin ƙasa, gwamnoni da takarar kujerun majalisun tarayya. Ana sa ran PDP ta gwada zurfin ruwa da abin da ya faru da ita a lokacin zaɓukan share-fagen zaɓen 2015 inda ya’yan jam’iyyar suka zarge ta da yin ƙarfa-ƙarfa wajen zaɓo waɗanda zasu riƙe mata tuta, kafar da APC ta samu damar shiga a zaɓen.
Masu kula da al’amurran siyasa sun yi hasashen cewa jiga-jigan jam’iyyar da dama ne ke hararen kujerar Aso Rock. Daga cikin su akwai Sanata Ahmed Makarfi, tsohon gwamnan Jihar Kaduna, kuma tsohon wakili a majalisar dattiɓai, da ya kasa kare kambin sa a zaɓen 2015. Bugu da ƙari kuma shugaban riƙon ƙwarya a PDP, bayan kai ruwa rana tsakanin sa da tsohon gwamnan Jihar Borno Ali Modu Sheriff dangane da shugabancin jam’iyyar.
Maƙarfi ya shiga jerin sunayen waɗanda ake kyautata zaton samun tikitin ɗan takarar jam’iyyar ne bisa ga dalilin iƙirarin da PDP tayi a baya na cewa ɗan takarar ta na 2019 zai fito ne daga arewa. Duk da akwai maza a gaban sa, cikin ‘yan kwanakin baya an jiyo shi a cikin wata tattaunawa da aka yi dashi a Legas yana cewa akwai yiwuwar yayi takarar kujera lamba ta ɗaya a Nijeriya. Duk da hatta nasarar da ya samu a babbar kotuñ ƙuli wasu masana na kallon ta a matsayin kura da shan bugu gardi da karɓar kuɗi.
A gaban Ahmed Maƙarfi, akwai tsohon gwamnan Jihar Jigawa-Alhaji Suleh Lamiɗo wanda ɗaya ne daga cikin ƙusoshin da suka kafa jam’iyyar PDP, tun a matakin farko. Mutun ne mai tsayayyar manufa a siyasance wanda ya buwayi guguwar sauyin da yayi tafiyar ruwa da takwarorin sa. Lamiɗon ya bayyana cewa, matuƙar jam’iyyar sa tare da ‘yan Nijeriya suka miƙo mashi goron gayyatar takarar shugabancin Nijeriya, babu abinda zai hana ya karɓa.
Kafin kotun ƙoli tayi waje-rod da Sanata Ali Modu Sheriff wajen kasancewa halastacen shugabancin jam’iyyar PDP, an yi hasashen cewa shi ma yana hararen kujerar shugaban ƙasa a cikin wannan zaɓe mai zuwa na 2019. Duk da ba a San abinda baya za ta haifa ba, amma ana kallon cewa wannan mafarki na Sheriff zai yi wuya ya kasance gaskiya; ganin an riga an ƙwace goriba a hannun kuturu.
A wani batu na daban kuma, a wannan gaɓar, har kawowa yanzu ba a iya tantance matsayin ‘yan sabuwar PDP ba; irin su Alhaji Atiku Abubakar, Sanata Rabi’u Kwankwaso, Murtala Nyako da Rotami Amechi da makamantan su, waɗanda daga baya suka shelanta sauya sheƙa zuwa sabuwar jam’iyyar APC? Mutanen da zafin ƙarfa-ƙarfar hana su takarar shugabancin ya tunzura sauya sheƙar, shin anya ba a sake rinawa ba kuwa? Baya ga wannan kuma, shin ko rikit-rikitar jam’iyyar a matakin jihohi zai bari ta iya taɓuka wani abu a zo a gani da haye siraɗi a wannan zaɓen mai zuwa?
Baya ga wannan halin rashin tabbas wanda ya yiwa jam’iyyar PDP ƙawanya, bata sauya zani a jam’iyya mai mulkin tarayyar Nijeriya ba, wato APC. Jam’iyya ce wadda mazubin tsarin ta da yanayin samuwar ta; tun da farin farko bai ba manazarta wahalar tsikayo tashar da za ta ci birki ba. A ƙidayar gwari-gwari, jam’iyyu ne masu ra’ayoyi da alƙiblu daban- daban ne suka haɗu wuri guda wajen ribibin bushiya da mai agalemi.
An ƙulla wannan auren bizar jam’iyyar APC ne a ranar shidda (6) ga watan Fabarairun 2013, a tsakanin jam’iyyun ACN da CPC haɗi da ANPP tare da wani ɓangare na APGA. Kana da bukin sa hannun curewa wuri guda daga ƙososhin kowanne ɓangaren jam’iyyun da suka shafi Mista Tom Ikimi a gefen ACN; sai Sanata Annie Okonkwo wanda ya wakilci APGA. Shi kuma tsohon gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya kasance madadin ANPP.
Amma cikin ƙanƙanin lokaci, kan kace kwabo Mista Annie Okonkwo da Tom Ikimi tare da Ibrahim Shekarau, tuni suka wancakalar da kayan baikon su, tare da sauya sheƙa zuwa PDP. Saɓatta-juyen wadda ta zo ta dalilin muhawarar da ta kaure dangane da matsayin riƙe jihohin da gwamnonin PDP waɗanda suka sauya sheƙa zuwa sabuwar jam’iyyar, wannan ya ɗora ɗan-ban marsala da shakkun alƙiblar jam’iyyar ta dosa.
Har wala yau, duk da yake siyasa ta gaji kama-in-kama, wasu na kallon tankiyar da ta ɓarke a tsakanin manyan ƙusoshin APC; da ya kai ga dole aka gudanar da zaɓen share fagen raba gardama a Legas, zaɓen da yaba Muhammadu Buhari nasarar ƙuri’u 3430 birbishin takwarorin nasa. Yayin da Dr Kwankwaso ya zo na biyu da ƙuri’u 974, sai Turakin Adamawa na uku da adadin mutane 954. Sauran sune Owelle Rochas Okoroch da Mista Sam Nda-Isiah na huɗu.
Duk da kuma yadda bayan bayyana sakamakon zaɓen , wanda ya ayyana Muhammadu Buhari ne ya lashe shi; kusan baki ɗayan ‘yan takarar sun sha alwashin yin aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin da Malam Buharin zai kafa idan yayi sa’ar karɓar gwamnati a hannun Dakta Jonathan, matakin da a lokacin wasu na ganin sa mai matuƙar wuya. Yayin da wani bincike ya nuna cewa da dama daga cikin ‘yan takarar gwamnoni, sun yi masa ingiza mai kantu ruwa ne. Amma dai ko ba komai wannan ya jawo dole gyaɗa tayi mai, idan kuma ta ƙi ta sha matsa.
Inda gizo ke saƙa shi ne, me nene matsayin Alhaji Atiku Abubakar, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, da makamantan su dangane da yanke shawarar sake tsayawar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari takara a 2019, ko zai haƙura? Akwai hasashen da yake cewa matuƙar Buhari yayi hannun-riga da muradun wasu daga cikin ƙusoshin jam’iyyar komi na iya wakana.
Binciken ya bankaɗo cewa ci gaba da zaman wasu jiga-jigai a cikin jam’iyyar ya ta’alaƙa ne da yadda matsayar shugaban ta kaya. Musamman tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Jihar Kano Dr Kwankwaso. Kuma ana kyautata zaton cewa hakan ne ma ya sa Buhari yayi gum da bakin sa.
A wani batu na daban kuma, dangane da wannan matsalar; idan tayi daren-kure, Turakin Adamawa yana iya juyawa tsohuwar jam’iyyar sa ta PDP matuƙar zai samu kafar tsayawa takarar shugabancin Nijeriya a 2019. Sabili da yadda Atikun ke kallon wannan ita ce damar kasancewar sa shugaban Nijeriya na gaba, inda ɗimbin magoya bayan sa daga yankin kudancin ƙasar nan ke ƙara masa karsashi.
Shi ma tsohon gwamnan Jihar Kano Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso yana da wannan burin a zuciyar sa wajen samun tikitin takarar shugabancin giwar Afrika. Yayin da wani bincike ya tabbatar da cewa ruwa a jallo Kwankwaso yake shauƙin cimma wannan burin nashi. Musamman yadda yake daɗa samun magoya baya, duk da taƙon-saƙan dake gauni tsakanin sa da wanda ya gaje shi.
Wani ƙusa a cikin jam’iyyar APC (National Working Committee) wanda ya ƙi yarda sunanan sa ya fito ɓalo-ɓalo ya bayyana cewa, hatta shugaban ƙasa Buhari ya san da wannan tubka da warwarar rikicin cikin gida da ya dabaibaye APC, kuma maganar tsayawar sa ko akasin hakan ne kaɗai zai nuna alƙiblar inda kan sitiyarin motar ya dosa.