Zaɓen 2019: Lamiɗo Ne Ɗan Takararmu –Alelu

Daga Umar Faruk, Birnin Kebbi

Shugaban ƙungiyar ‘Credible Alternatiɓe’ ta ƙasa, reshen Jihar Kebbi, Alhaji Halliru Alelu a ƙarkashin jam’iyyar PDP reshen Jihar Kebbi ya bayyana cewa zaɓe mai zuwa na shekarar 2019, Sule Lamiɗo tsohon Gwamnan Jigawa su ke so a matsayin ɗan takarar shugaban Nijeriya a jam’iyyar su ta PDP.

Alhaji Haliru Alelu ya bayyana haka ne a lokacin da ƙungiyar su ta ‘Credible alternatiɓe’ ta gudanar da wani taron gana wa da shi, Dakta Sule Lamiɗon da muƙarrabansa a Otal ɗin Saffar  dake cikin unguwar Gesse a garin na Birnin-kebbi, wanda aka gudanar cikin makon da ya gabata.

Har  ila yau , ya ce ƙungiyar na fafutukar tsayar da ɗan takara  na gari  da cancanta yasa suka yanke shawarar neman   cewa jama’ar jihar kebbi da ‘yan ƙasar mu Nijeriya da su ba ƙungiyar su da credibly alternatiɓe a karkashin Jam’iyyar PDP don Lamido ya zamo dan  takarar shugabancin  Nijeriya .

Kazalika ya ce dalilin  son Dakta Sule Lamido ya zamo dan takara domin  ƙasar mu Nijeriya ta samu zama abu guda da wasu manyan  ƙasashen da suka cigaba ta fuskar tattalin arzikin ƙasa da wanzuwar dimokraɗiyya a ƙasashen su.

Ya ce, ci gaba da cewa tsohon Gwamnan na jigawa zaya iya shugaban cin Ƙasar nan saboda tarihin sa  kan mukaman da yarike a ƙasar nan kama tun  daga Dan majalisa da yayi tun  ana legas har mulki sa  a jihar jigawa shekaru takwas, kuma yayi fice  a ƙasar Nijeriya kai har ma ƙasashen waje.

Daga nan ya ƙara da bayyana wa wakilan Sule Lamiɗo da suka halarci taron nasu na neman goyon bayan da hadin  kai kan tabbatar da cewa Sule Lamido ya tsaya takarar shugaban cin ƙasar Nijeriya a zaɓen  shekara ta 2019. Saboda haka ya ce  sako ne ya aikewa Sule Lamido domin ya fito kan Neman shugaban cin ƙasar nan, domin shine ra’ayin su a 2019.

Shima da yake  gabatar da jawabin sa  Dakta  Sule Lamido kuma  tsohon Gwamnan jihar jigawa, Wanda Alhaji   Umar KyNijeriya i “duk jihohin da suka ziyarta in banda jihar Jigawa basu ga jihar da tafi tsari mai kyau ba da ba da goyon baya ga Sule Lamido ba tare ya neman ba sai ga jihar Kebbi” , ya ci gaba da cewa  sunzo jihar kebbi ne domin su yi zumunci su sadu da masoyan Dakta Sule Lamido, ya ce,  da yardar Allah da zaran sun koma Jigawa zaya isar da takardar neman   Sule Lamido ya tsaya takarar shugaban cin ƙasar nan a shekara ta 2019 a Nijeriya da ƙungiyar credible alternatiɓe a karkashin Jam’iyyar PDP a jihar ta kebbi kan kira ga  tsohon Gwamnan cewa shine dan  takarar su na Shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa.

Har  ilayau, kyari ya bayyana jinda din sa  ga  irin  abin da ya gani a wurin taron  ganawar da aka gudanar a saffar otel  dake Birnin-kebbi, ya nuna cewa Dakta Sule Lamido yana da masoya a jihar ta kebbi sosai.

Hakazalin Alhaji Umar kyari ya ba da hukuri ga  masoyan na tsohon Gwamnan jihar ta jigawa domin ya so ya halarci wannan gagarumin taron  nuna goyon bayan ƙungiyar credible alternatiɓe ta jihar kebbi ga  fitowa takarar shugaban cin ƙasar nan. Domin wasu abubuwa da suka fi karfin sa  ne suka hana shi zuwa jihar ta kebbi domin ya ansa kiran da ƙungiyar ta yimasa a jam’iyyance.

Daga nan ya gode  wa  shuwagabanin ƙungiyar kan soyayar da aka nuna wa  tsohon Gwamnan Sule Lamido na jihar jigawa suna godiya kwarai da gaske.

 

Exit mobile version