Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Za A Aurar Da Zawarawa 100 A Karamar Hukumar Argungu

by
4 years ago
in RAHOTANNI
3 min read
Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Ci Rayuka 18 A Kebbi
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Daga M.J. Yusuf, Birnin Kebbi

Yanzu haka dai shirin aurar da zawarawa guda dari (100) a karamar hukumar mulkin ta Argungu ya iso gaba ta karshe India ta kai ga yanzu an kai ga matakin gwajin lafiya angwayen tare da amaren su.

Alhaji Aminu Musa Magajin gari wanda shi ne ke wakiltar mai martaba Saukin Kabin Argungu Alhaji Samaila Muhammad Mera a harabar hedikwatar karamar hukumar mulki ta Argungu, ya bayyana gamsuwar  sa bisa ga yadda marasa hali daga cikin matasa da kuma wadansu masu dan yawan shekaru suka masa wannan kira kuma suka amince da ka’idojin da duk aka shata.

Labarai Masu Nasaba

Hukumar Alhazan Kogi Ta Fara Shirin Bita Ga Maniyyata

Fashewar Gas A Kano: Ministar Jinkai Ta Nemi A Dauki Matakan Riga-kafi

Ya cigaba da cewa wannan shirin fa an aiwatar d shi ne bisa ga zummar rage bata-gari musamman abin da ya shafi zinace- zinace a cikin alu’umma da tallafawa ga marasa karfi, kuma yana iya zamewa wata sila ta saukaka aure,  Hasali ma yana iya zama ishara ga iyayen da ke tsawwalawa wajen aurar da yayan su, ya Allah budare ne ko zawarawa.

Malam Abdullahi Haruna Tambasi (Mai gwauraye) wanda shi ne saukin gwaurayen Kabi ya bayyana wa wakilin mu da cewa wannan abin alfahari ne da jin dadi a ce wani alheri ya sauka a cikin al’ummar da ka ke jagoranci. Wannan shirin ya dade da kafawa tun gwamnatocin da suka gabata amma sai dai romon baka abin ya zamo Kaulin-bi-la-amalin sai da wannan gwamnati ta Atiku Bagudu ta zo ta aiwatar da shi.

Ya cigaba da cewa yanzu haka akwai zawarawa sama da dubu biyu da suka jiran irin wannan damar saboda haka in-sha-Allahu da zarar aka kammala wannan a matsayin gwaji za a cigaba da wani.

Ya kuma na kunnen zawarwan da su kasance masu biyayya ga mazajen su sannan kuma su yi tanadin kudin da aka ba su a matsayin jari su nemi sana’o’i kada su saka kudin a gaba su kashe.

Daga karshen ya yi farar Allah ya saka wa duk wanda ya taka wata rawa wajen ganin an sami nasarar wannan shirin.

Honorabul AbdulSalam Sani, mai magana  da yawun shugaban karamar hukumar mulkin ta Argungu Alhaji Musa Muhammad Tungulawa ya bayyana cewa samun  nasarar wannan shirin ya samo asali ne ta hangar hadin gwiwar karamar hukuma da masarauta da kwamitin hisba da kuma sarkin gwauraye.

Ya cigaba da cewa wannan shirin ba shakka ya sani nasara duk da ya ke ba za a rasa yana matsaloli ba musamman wajen wadansu mazaje da adadin su bai kai uku bisa dari ba a lokacin da suka ji an ce sai an yi gwaji sai kuma wadanda suka zo don su karbi kudin wadanda a zaton su kudin ne za a ba su sai suka fita wanda bai hana  samun nasarar shirin ba.

Malama Sadiya  Isah daya daga cikin zawarawan da suka kammala gwajin tantance lafiya zawarawan kuma wacce ta yi watanni takwas kacal yana zawarci ta bayyana jin dadin ta kuma ta yaba wa hukuma bisa kirkiro wannan shiri da ta yi na shirya auren kuma bayan shirya auren ga wani tallafi na jari don su tsaya da kafafuwan su.

Ta yi kira ga zawarawan da ke jan kafa wajen kawo mazajen aure da kuma wadanda ke jin kunyar shiga wannan shirin da su sake tunani saboda a rayuwar ya mace ba abin da fi a wajen ta da ya kai yana gidan aure komai matsayin gidan su.

ADVERTISEMENT

Malam Garba Usman, daga daga cikin wadanda za su angwancewa ranar 17/3/2018 ya bayyana farin cikin sa Inda ya ce shi ba ya da matsala wajen saka mata amma sai dai tsadar auren ce ta fi damun sa. Ya ce wannan ta isa ta zamo yar manuniya ga mata da kuma iyayen da ke tsawwalawa wajen aure.

Ita kuwa Malama Fatima Ibrahim wace ta share shekaru sama da da goma ta na zawarci ta bayyana wannan shirin a matsayin wata rahama ga resu, ta dai ja kunnen mazajen su da su yi hakuri da su kuma su rike amana.

Shugabanci majalaisar Malamai ta karamar hukumar mulki ta Argungu Dokta Abubakar Muhammad Wali ya yaba wa gwamnati bisa ga wannan shirin da bullo da shi wanda kuma dauke wani nauyi ne da shari’a ta dora wa mahukumtana na yin duk abin da ya shafin wani bangare na rayuwa.

Ya kuma yi kira ga yana kwamitin da aka dorawa alhakin tantace ma’auratan da su ki tsoron Allah kada su saka siyasar a cikin.

 

Like this:

Like Loading...
Tags: Aurar Da Zawarawa
SendShareTweetShare
Previous Post

Dan Majalisar Dattawa A Kebbi Ya Raba Injinan Noma A Mazabarsa

Next Post

Tsakanin Gwamna Abubakar Da Ahmed Yarima: Siyasar Cigaba Ko Akasi?

Labarai Masu Nasaba

Hukumar Alhazan Kogi Ta Fara Shirin Bita Ga Maniyyata

Hukumar Alhazan Kogi Ta Fara Shirin Bita Ga Maniyyata

by Ahmed Muhammad Dan'asabe
3 days ago
0

...

Fashewar Gas: An Zakulo Gawarwaki 9 A Ginin Da Ya Rushe A Kano

Fashewar Gas A Kano: Ministar Jinkai Ta Nemi A Dauki Matakan Riga-kafi

by
3 days ago
0

...

Baki Biyu Bai Dace Da Matsayin Amurka Ba

Baki Biyu Bai Dace Da Matsayin Amurka Ba

by CMG Hausa
3 days ago
0

...

Fashewar Gas: An Zakulo Gawarwaki 9 A Ginin Da Ya Rushe A Kano

Fashewar Gas: An Zakulo Gawarwaki 9 A Ginin Da Ya Rushe A Kano

by
5 days ago
0

...

Next Post
Gwamnatin Bauchi Ta Himmatu Wajen Samar Wa Matasa Guraben Aiyukan Yi, In ji HOS

Tsakanin Gwamna Abubakar Da Ahmed Yarima: Siyasar Cigaba Ko Akasi?

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: