Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya amince da daukar daliban jami’ar UMY aikin gwamnati wadanda suka gama karatu da maki mafi girma a matakin digiri na daya (first class). Ya ce hakan nada nufin tabbatar da ganin matasa maza da mata masu hazaka sun shiga cikin aikin gwamnati don a samu ci gaba.
Gwamnan ya bayyana cewar a wajen taron nuna hazaka a Jihar Katsina na kasa mai nufin zakulo hazikan matasa da ya gudana a hedkwatar daukar ma’aikatan kananan hukumomi ta Jihar.
Ya ce gwamnatin shi ta ba bangaren ilimi fifiko don tabbatar da cigaba. Kamar yadda yace bullo da jarabawar kwalfayin da gwamnatinshi tayi ya haifar da da mai ido. Ya yi nuni da cewa a shekarar (2019) Jihar Katsina ta zama zakara a gasar muhawara ta shugaban kasa ya kuma kara da cewa yanzu haka Jihar na cikin gasar ta wannan shekara.
Gwamnan ya kuma yabama wadanda suka shiga gasar zakulo hazakan sai ya yi fatan cewa za a yi adalci wajen zaben wanda ya fi daga cikin wadanda suka fito cikin gasar.
A wani labari makamancin wannan majalissar dokokin Jihar Katsina ta zartas da dokar shekarun aje aiki ga malaman da ke shiga aji da wadanda basu shiga aji na kwalejin kimiyya ta Hassan Usman Katsina daga shekaru (65) ko kuma shekaru (40) ana aiki.
Majalissar zartaswar ta mika kudurin dokar ga majalissar domin a yi mata garanbawul domin ta samar da shekaru (40) ana aiki ko kuma cimma shekaru (65) da haihuwa ga ma’aikatan da basu shiga aji na kwalejin.
Matakin ya biyo bayan nazarin rahoton kwamitin kula da lamurran ilimi mai zurfi. Jagoran majalissar Abubakar Suleiman Abukur ya gabatar da kudurin dokar aka yi mata karatu na (3).
Mataimakin shugaban majalissar injiniya Shehu Dalhatu tafoki wanda ya jagoranci zaman majalissar na wannan Larabar ya bayyana cewa zartas da dokar na daya daga cikin nasarorin da gwamnatin APC ta samu a jihar dama majalissar dokoki mai ci yanzu.
Injiniya Shehu tafofi ya ce ma’aikatan da basu shiga aji na manyan makarantun gaba da sakandire a jihar nan, na daga cikin masu ruwa da tsaki wajen tafiyar da sha’anin mulki na irin wadannan makarantu.
Tun da farko, shugaban kwamitin Shamsuddeen Abubakar Dabai wanda ya gabatar da rahoton ya roki majalissar da ta amince da dukkanin garanbawul din da aka yima dokar ta 2017.