Daga Zubairu M Lawal,
Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya kaddamar da kwamiti don yin bincike kan dalilin da ya sa kananan hukumomin jihar ba sa iya biyan albashin ma’aikata a mataki na uku na gudanar da mulki. An kafa Kwamitin mai mambobi shida ne a dakin taro na Ma’aikatar Kananan Hukumomi, da yankin raya kasa da Harkokin Masarautu Gargajiya ta jihar a ranar Juma’a.
Da yake kaddamar da kwamatin Gwamnan ya umarce su da su binciki lamuran da suka shafi gazawar kananan hukumomi a jihar, ta yadda za a aiwatar da biyan albashin ma’aikatansu. Gwamnan ya ce ya lura majalisun, kananan hukumomi suna fuskantar matsalar batun albashin Ma’aikata duk da cewa suna mataki na uku cikin tsarin Gwamnati.
Injiniya Sule ya ambaci basussukan fansho da aka biya, biyan kashi da kashi da sauransu, a matsayin shaidar gazawa daga bangaren kananan hukumomi wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora musu, lamarin da ya haifar da yanke kauna da rashin jin dadi tsakanin ma’aikatan kananan hukumomi. Dangane da wannan cigaban, gwamnan ya tuno da sadaukarwarsa yayin da yake daukar nauyin shugabanci a jihar, don magance matsalolin da ke faruwa na yawan biyan albashi, bashin fansho da yawan albashin da ya wuce kima.
Injiniya Sule ya bayyana cewa kafa kwamitin binciken ya zama dole ne saboda bambance-bambancen da ake gani da kuma matsalolin da ba za a iya sasantawa ba wadanda ke bukatar a gano, domin dawo da hankali da kuma yadda aka saba a tsarin kananan hukumomin. Kwamitin, wanda ke da sharuda shida, zai kasance tare da wasu, zai binciki gaskiya ko akasin haka kan zarge-zargen da ake yi wa DPMs da DFAs na majalisun kananan hukumomi, da kuma yankunan raya kasa na rashin biyan albashin ma’aikata .
Haka nan zai binciki hanyoyi da nakasu a cikin shirye-shiryen biyan bashin alabashi na takardu albashin daga 2012 zuwa yau. A wani bangare na kudurin gwamnatinsa na gabatar da tsafta a tsarin kananan hukumomin, gwamnatinsa ta kammala shirye-shirye domin biyan bashin wata daya ga ‘yan fansho don rage radadin wahalar da suke sha, ta amfani da kaso na biyu na kudaden SIFTAS.
Gwamnan ya umarci membobin kwamitin, wadanda aka zaba bisa ga kwarewarsu da aiki tukuru, da su zauna a sama da ka’idojin da aka ba su. “Dole ne ku gudanar da aikinku yadda ya kamata, ba tare da wani tunani ko son kai ba,” in ji shi. Shi ma a jawabinsa na godiya, Shugaban kwamitin binciken, Mista Ishaya Agidi Awotu, ya lura cewa rashin bin ka’idoji wajen tafiyar da harkokin kudi, ya samo asali ne sakamakon rashin karfi na cikin gida. Yayin da yake yaba wa gwamnan kan kokarin da ya yi na kiyaye kadarorin jihar, shugaban kwamitin ya ba da tabbacin membobin za su gudanar da aikin da matukar muhimmanci.