Daga Khalid Idris Doya
Gwamnatin Tarayya ta ayyana cewa na kusa za ta bude iyakokinta bayan gamsuwa da matakan da ta so cimmawa kan dalilinta na kulle iyakokin tun da farko.
Idan za ku iya tunawa dai iyakokin Nijeriya sun kasance a kulle ne tun watan Agustan 2019 domin dakile yawaitar shigo da miyagun kwayoyi, dakile shigo da makamai da kuma kokarin bunkasa albarkatun gonan da muke nemowa a cikin Nijeriya hadi da rage yawan shigo da kayan da kasashen makwafta ke sarrafawa domin bai wa kasar damar sarrafa nata da kanta.
Zainab ta shaida cewar kwamitin da shugaban kasa ya kafa kan batun ya bada shawarorin a sake bude iyakokin kasar nan.
Ta ce, nan kusa kadan kwamitin zai gabatar da rahotonsa wa shugaban kasa Muhammadu Buhari daga bisani kuma a sanar da batun a hukumance.
Tun bayan dai da Nijeriya ta kulle iyakokinta kungiyoyi daban-daban sun ta kiran da a sake bude iyakokin suna masu bada dalilansu mabanbanbanta.