Connect with us

LABARAI

Za A Ci Tarar Naira 5,000 Ga Wanda Ya Karya Dokar Hana Zirga-zirga

Published

on

Daga yanzu duk wanda aka cafke da karya dokar haramta bada tazara a tsakanin jama’a da wanda aka cafke da karya dokar hana fita za su biya tara dubu biyar-biyar a jihar Bauchi.

Inda za a kafa kotun tafi da gidanta da za ta ke yanke hukunci ga wadanda suka take dokar.

Gwamnan jihar Bala Muhammad ya sanya hannu kan sabon dokar a yau wanda gwamnatin jihar ta shaida cewar ta dauki matakin ne domin kare yaduwar cutar Korona a jihar.

Gwamna Bala ya ce daga yanzu, dole ne jama’a su bi umurnin haramta fita a ranakun da gwamnatin ta ware domin zaman gida, inda sabon dokar ya nuna duk wanda ya karya dokar zai biya tarar dubu 5,000.

“Masu aiyuka na musamman su za su fita domin gudanar da aikinsu, amma wajibi ne duk wanda yake kan aiki na musamman zai sanya takunkumin rufe hanci da baki (Face Masks) muddin aka kama mutum bai sanya ba zai biya tarar dubu 5,000,” A cewar sabon dokar.

Har-ila-yau, duk wanda aka kama yana sana’ar Achaba zai biya tarar naira dubu biyar.

Duk wanda ya karya dokar sana’ar Keke-Napep da aka kama da daukan mutum fiye da biyu a lokaci guda zai biya tarar dubu goma, sai kuma masu motocin da suka saba dokar da gwamnatin jihar ta sanya za su biya tarar dubu 20,000, masu motar ‘Bas–Bas da suka karya dokar gwamnatin su ma za su biya tarar dubu 20,000, sai kuma masu manyan motoci Tiraktoci idan aka kama mutum da karya dokar hana shigowa jihar za a ci tararsa dubu 30,000

Gwamnan ya bada umurni mai karfi ga Babban Jojin jihar da a tabbatar da aiwatar da sabon dokar nan take, inda ya kuma umurci a tilasta amfani da dokar da majalisar zartaswar jihar ta fito da shi.

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad Abdulkadir ya tarraba hannu kan sabon dokar tare da cewa hakan zai kai ga tilasta jama’an jihar bin umurni da matakan gwamnati kan yaki da cutar Korona.

Da yake jawabi bayan sanya hannu kan sabon dokar gwamna Bala ya shaida cewar sun fitar da dokar da za su kai ga hana yaduwar cutar a tsakanin jama’a, don haka ne ya ce majalisar zartaswa na jihar ta fitar da matakan da za su tilasta wa jama’a bin dokokin da matakan da gwamnatin jihar ta samar domin kiyaye yaduwar cutar.

“Mun kawo wadannan dokokin ne domin a kowani lokaci muna son muke tafiyar da komai bisa doka da oda, ya jawaba a garemu mu fitar da abubuwan da muke son cimmawa, mun sanya dokar hana zirga-zirga mai sauki ga jama’a, mun rufe kasuwanni na wasu ‘yan kwanaki, mun haramta sana’ar Achaba kwata-kwata, mun takaita yawan mutanen da za a ke dauka a cikin Keke-Napep, sannan kuma mun haramta dukkanin tarukan jama’a,”

“Mun yi amfani da dukkanin hankalanmu domin sauke nauyin da ke kanmu, duk da ba za mu ji dadin duk wani da hakan ba zai mishi dadi ba, amma dai muna daukan wadannan matakan ne domin kare rayuka da lafiyar jama’an jihar Bauchi,” A cewar gwamna Bala Muhammad.

Gwamna Bala ya shaida cewar an cafke mutane 100 da suka shigo jihar Bauchi daga wasu jihohi masu gayar fuskantar matsalar Korona, sai ya ce za su ci gaba da tabbatar da killace iyakokinsu domin kiriya daga cutar.

A tasa bangaren Antoni Janar kuma kwamishinan shari’a na jihar, Barista Yakubu Bello Kirfi, yayi bayanin cewar sabon dokar na zuwa ne a sakamakon annobar korona.

Ya ce, Gwamnatin Bauchi ta dauki matakan da suka dace domin kare rayuka da lafiyar jama’an jihar.
Advertisement

labarai