Za A Cire Wa ‘Yan Kasuwar Da Suka Yi Gobara A Katsina Tallafi Daga Albashin Ma’aikatan Jihar

Zaman Lafiya

Daga Sagir Abubukar,

Majalisar Zartaswar Jihar Katsina, karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta amince a cire wa kowane ma’aikacin gwamnatin jihar da na kananan hukumomi talatin da hudu da malaman makaranta wani kaso daga cikin albashinsu, domin bai wa ‘yan kasuwar babbar kasuwar Katsina gudummawa.

Kwamishinan Shari’a na jihar Katsina, kuma shugaban Kwamitin Aiwatar da aikin kwamitin da gwamnatin jIhar Katsina ta kafa, Barista Ahmad Usman El-marzuk ya bayyana wa manema labarai hakan, bayan kammala zaman majalisar zartaswa da gwamna Aminu Bello Masari ya shugabanta a yau Laraba a gidan gwamnatin jihar Katsina.

Barista Ahmad Usman El-marzuk ya kara da cewa za’a cire kaso ukku cikin dari daga Ma’aikaci dake mataki na daya zuwa mataki na goma sha hudu. Haka zalika, za’a cire wa gwamna da Kwamishinoni da masu baiwa gwamna shawara da masu taimaka masa na musamman da kuma sauran masu rike da mukaman Siyasa, za’a cire masu kaso ashirin na albashinsu cikin dari.

Da ya juya kan tallafin da guddumuwar da yan kasuwar babbar kasuwar Katsina suka samu, an samu naira Miliyan 152, wasu sun shigo hannu, Wasu kuma ba su kai ga zuwa hannu ba. Kwamitin ya gano yan babbar kasuwar Katsina sun yi asarar naira Miliyan dari tara da biyu, jimlar asarar da gobarar ta haifar.

Exit mobile version