Tsohon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Andries Iniesta, ya bayyana cewa idan shugabannin kungiyar basu tashi tsaye ba zasu dade basu shawo kan matsalar kungiyar ba.
Kakar kwallon kafa ta bana ta nuna rashin kokarin Barcelona a gasar cikin gida, amma tana haskakawa a gasar cin kofin zakarun turai ta Champions League ta kakar wasa ta 2020 zuwa 21 wadda ake bugawa.
Kungiyar ta Barcelona tana yin rashin nasara a hannun kungiyoyin da bai kamata su doke ta ba a bana da hakan ke nuna cewar abune mai wahala idan tana cikin wadanda ake sa lashe kofin La Liga na bana.
Ranar Asabar Cadiz ta doke Barcelona da ci 2-1 a wasan da suka fafatawar da suka yi a filin Ramon de Carranza sai dai za’a iya cewa baa bin mamaki bane saboda Cdiz din itace ta doke Real Madrid a kwanakin baya.
Kawo yanzu Barcelona tana ta takwas a teburin La Liga da maki 14, bayan buga wasa 10 a kakar bana bugu da kari kungiyar wadda mai koyarwa Ronald Koeman ke jan ragama ta ci wasa hudu a La Liga da canjaras biyu da rashin nasara hudu da kwantan wasa.
Barcelona ta yi rashin nasara a wasanni da dama a bana kamar yadda ta yi a shekarar 2017 zuwa 2018 da kuma 2018 zuwa 2019 a La Liga, yayin da ta yi rashin nasara a wasa uku ta kuma lashe kofin a shekarar 2018 zuwa 2019.
Sai dai kuma Barcelona tuni ta kai zagaye na biyu a gasar Champions League ta bana da maki 15, yayin da Jubentus take ta biyu da maki 12 a rukuni na bakwai kafin su fafata a wasan yau aga wadda zata zama jagora a rukunin nasu.
A kakar shekarar 2003 Enric Reyna shi ne ya rike Barcelona a matakin rikon kwarya, bayan da Joan Gaspart ya yi murabus daga baya Radomir Antic ya maye gurbin Louis ban Gaal a matakin koci.
A waccan kakar Barcelona ta fuskanci kalubalen samun gurbin shiga gasar UEFA Cup, inda kungiyar ta sa kwazo ta kuma samu gurbin a wasan karshe da ta buga, sannan kuma a lokacin Laporte ya kalli karawar a matakin shugaban kungiyar a lokacin da ya ci zabe ya zama jagora na hudu a kungiyar a kakar.
A kakar wasa ta 2020 zuwa 21 za ta kammala ne da shugaba uku, bayan Josep Maria Bartomeu sai Carles Tuskuets na rikon kwarya da wanda za a zaba ranar 24 ga watan Janairun shekara ta 2021.
Hakika Barcelona na bukatar sa kwazo a kakar bana ko dai ta lashe La Liga ko kuma ta ci Champions League, bayan da Kyaftin din kungiyar Lionel Messi a ke rade-radin zai bar Camp Nou a karshen kakar bana.