Nakasassu Dubu daya Da dari Shida ne za su amfana da shirin bai wa matasa ayyukan yi na watanni uku na gwamnatin tarayya a Jihar Kwara.
Shugaban kwamitin shirin a Jihar, Oluwasegun Oyewo, ne ya bayyana hakan a bayan da ya yi wata ganawa da hadaddiyar kungiyar shugabannin masu nakasa a Jihar, in da ya ce wannan adadin yana daidai ne da kashi 10 na mutanan da za su amfana su 16,000 a shirin cikin Jihar.
Ya kara da cewa, mutane 1,000 ne za a dauka daga kowace karamar hukuma cikin kananan hukumomin Jihar 16. Wadanda kuma za a dauka din tilas ne su kasance a tsakanin ‘yan shekaru 18 zuwa shekaru 50, sannan tilas ne kashi 20 daga cikinsu su kasance masu ilimi ne, hakanan kaso 30 a cikinsu lallai su kasance mata ne.
Oyewo ya ce ba lallai ne wadanda za a daukan su kasance ‘yan asalin karamar hukumar ba, amma tilas ne su kasance mazauna karamar hukumar ce. Ya kara da cewa, ba kuma lallai ne wadanda za a daukan su kasance sun iya wata sana’a ba.
A cewar sa, za a fara gudanar da shirin ne daga watan Oktoba zuwa watan Disamba, 2020, za kuma a rika bai wa wadanda suke a cikin shirin tallafin naira 20,000 a kowane wata.
Sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, wanda Malam Salihu Balogun ya wakilce shi, ya yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, a kan samar da ayyukan yi ga matasa 774,000 a cikin shirin, wanda ya kwatanta da cewa abin a yaba ne.
Annobar Sace Farfesoshi Ta Kunno Kai A Arewa
An Sace Farfesa, An Kashe Dansa Da Mutum Uku A...