Khalid Idris Doya" />

Za A Daure Duk Wanda Aka Kama Da Yi Wa Mata Kaciya A Sudan

Kasar Sudan ta sanya yi wa mata kaciya cikin jerin manyan laifuka a kasar, tare da tanadin daurin shekara uku ga duk wanda aka kama na aikata al’adar, kamar yadda sabuwar dokar da aka sauya ta zayyana.

Kamfanin Dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa an tabbatar da sauya dokar zuwa cikin jerin manyan laifuka ne a ranar 22 ga watan Afrilu.

Sudan na daya daga cikin kasashen Afrika da aka yi amanna da kaciyar mata a kusan baki dayan kasar.

Akalla kasashen Afrika 27 ne ke yin wannan al’ada ta kaciyar mata a nahiyar, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.

Amma tuni wasu kasashen da dama suka haramta wannan al’ada wadanda suka hadar da Kenya da Mali da Liberia da Benin da Burkina Faso da kuma Central African Republic.

Sauran sun hada da Chadi da Côte d’Ivoire da Djibouti da Masar da Eritrea da Habasha da Ghana da Guinea da Guinea-Bissau da Niger sai kuma Nijeriya.

Exit mobile version