Connect with us

LABARAI

Za A Fara Aiki Da Mafi Karancin Albashi Zuwa Karshen Shekara –NLC

Published

on

Babban sakataren kungiyar kwadago ta kasa (NLC), Mista Peter Ozo-Esan, ya tabbatar wa Ma’aikatan kasan nan da cewa za a fara biyan su sabon tsarin albashi kafin karshen wannan shekarar.
Peter Ozo-Esan, ya bayar da wannan tabbacin ne cikin wata tattaunawa da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa ranar Talata a Abuja.
A cewar shi, duk da tsaikon da aka samu saboda hutun Sallah, kwamitin da ke tattauna lamarin mai kusurwa uku, zai kammala duk tattaunawar na shi ne a ranakun 4 da 5 ga watan Satumba.
“Muna sa ran ainihin ranar da aka tsayar ta fara amfani da sabon albashin a watan Satumba za ta tabbata.
“Ma’aikatan kasan nan za su ci gaba da neman hakan daga gwamnati, da zaran kuma an mika rahoton, kamata ya yi gwamnatin ta yi abin da ya dace na mika shi ga Majalisun tarayya domin hakan ne ya kamata a yi.
Kan damuwar da gwamnatocin Jihohi suke nu na wa a kan hakan, Peter Ozo-Esan, ya bayyana cewa, ai ba su ne za su ce ga abin da za su biya ba, a matsayin su na wadanda suka dauki ma’aikata tilas ne su yi aiki da sabon tsarin alabashin da doka ta amince da shi.
“Ba gwamnati ne ake sanya wa ma fi karancin albashi ba, duk masu daukan ma’aikata a cikin kasa ne ake sanya wa ma fi karancin albashin.
“Batun abin da gwamnonin Jihohi suke so ba shi ne ba, don wannan ba maganan siyasa ne ba, ma fi karancin albashi shi ne abin da ya kamata duk wani ma’aikaci a cikin kasa ya karba, ba a kuma yarje wa duk wani mai daukan aiki ya biya kasa da hakan ba.
“Muna kuma yin kira ga ‘ya’yan kungiyarmu da su mallaki katunan jefa kuri’unsu, domin su yi waje da duk wani gwamnan da ya nu na ba zai iya yin mulkin ba,” in ji shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: