Gwamnatin Jihar Kano za ta fara kama wadanda ke yawo ba tare da sanya takunkumin fuska ba wato (Face Mask) da ga ranar Laraba mai zuwa.
An bayyana dawo da dokar sanya takunkumin ya biyo bayan sake barkewar cutar Korona a Jihar Kano dama kasa baki daya.
A cewar mashawarci na musamman kan kafafen sadarwa na zamani ga Gwamnan Jihar Kano Salihu Tanko Yakasai, yace dama dokar ba sabuwa bace, kuma Gwamnati ba tace ta janye ba, jama’a ne dai kawai suka yi watsi da ita.
Ya ce, ya zama dole a dowa da dokar, duba da yadda annobar ta sake kunno kai, domin a kubutar da jama’a da ga hadarin kamuwa da cutar da kuma yadawa jama’a.
“Gwamnatin Jihar Kano taga ya kamata a dawo da dokar sanya takunkumin fuska, da kuma bada tazara tsakanin mutane, la’akari da barkewar korona a karo na biyu.
“Ya ce wannan umarni na Gwamnati ya fara aiki ne nan take, duk wanda bai sanya ba za a dauki mataki mai tsananin a kansa” A cewarsa.
Haka zalika wata sanarwa da ke yawo a kafafene sada zumunta na zamani na nuna cewa za a fara kamen wadanda basu da takunkumin fuskar ne daga ranar Laraba mai zuwa.