Za A Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomi 5 Ga Disamba A Yobe

Hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Yobe, (SIEC) ta ayyana shirin gudanar da zaben kananan hukumomin jihar a ranar 5 ga Disamban 2020.

Shugaban hukumar a jihar Yobe Dr. Mamman Mohammed, shi ne ya sanar da hakan a taron ma su ruwa da tsaki hadi da jam’iyyun siyasa daban-daban, da safiyar ranar Talata, a ofishin hukumar da ke Damaturu.
Hara zalika kuma Dr. Mamman ya kara da cewa wannan taron shi ne somin-tabi dangane da kankamar shirye-shiryen gudanar zaben wanda zai wakana watanni uku ma su zuwa.
A hannu guda kuma ya bukaci yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban cewa su fara gangamin zawarcen magoya baya, tare da shan alwashin cewa hukumar zaben za ta yi aiki da kowace jam’iyyar siyasa a jihar babu bambanci ko son kai.
“Saboda haka kuma gudanar da zabe mai tsabta, adalci, da gaskiya, akwai bukatar samar da kyakkyawan yanayi tare da sakarwa kowa mara domin taka muhimmiyar rawar da ya dace da doka da oda a siyasance.
“Wanda bisa ga hakan ne ma ya jawo mu ka taru a nan cikin yanci don mu tattauna hanyoyi da abubuwan da za su taimaka wajen gudanar da sahihin zabe mai cike da adalci, kana kuma muhimmin abu zaben ya kasance karbabbe ga kowa a wannan jihar ta mu,” in ji shi.

Exit mobile version