Jamila Zhou Ta CRI" />

Za A Hana Amfani Da Maganin Fentanyl A Kasar Sin

Yau Litinin ma’aikatar tsaron jama’a ta kasar Sin da hukumar kiwon lafiyar kasar da hukumar kula da kuma sa ido kan magungunan sha ta kasar sun fitar da wata hadaddiyar sanarwa cikin hadin gwiwa, inda suka bayyana cewa, tun daga ranar 1 ga watan Mayun bana, za a shigar da Fentanyl a cikin jeren sunayan magungunan sha da aka haramta yin amfani da su yayin jinya marasa lafiya, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin za ta sanya Fentanyl cikin jerin miyagun kwayoyi.

Kasar Sin ta shiga mawuyacin hali a baya sakamakon miyagun kwayoyi, a don haka har kullum tana mai da hankali matuka kan manufar yaki da miyagun kwayoyi, haka kuma ta samu sakamako mai gamsarwa wajen hana yaduwar Fentanyl a fadin kasar.
Kana matakin da kasar Sin ta dauka ya shaida wa kasashen duniya cewa, gwamnatin kasar Sin tana yaki da miyagun kwayoyi yadda ya kamata, haka kuma tana taka muhimmiyar rawa kan aikin yaki da miyagun kwayoyi tare da sauran kasashen duniya.
Kamar yadda aka sani, Fentanyl maganin hana jin zafi ne, ya ninka Heroin karfi har sau 50, kana ya ninka Morphine sau 100. A cikin ‘yan shekarun da suka gabata, an fara tace sabon nau’in miyagun kwayoyi ta hanyar yin da amfani da Fentanyl a Amurka da Canada da sauran kasashen duniya, adadin mutanen da suka rasa rayuka sakamakon shan irin wannan miyagun kwayoyi shi ma ya karu matuka, misali cibiyar magance da kuma yaki da cututtuka ta Amurka ta fitar da wani rahoto cewa, gaba daya adadin mutanen da suka mutu sakamakon shan Fentantl ya kai 18335. Amma Amurka ba ta dauki matakin da ya dace na dakile matsalar ba, sai dai ta rika suka cewa, Fentanyl ya samo asali ne daga kasar Sin.
Hakika kasar Sin ta dade tana gudanar da hadin gwiwa tsakaninta da Amurka kan matakan yaki da Fentanyl, misali a taron musanyar bayanan yaki da miyagun kwayoyin da aka kira a watan Oktoban shekarar 2017, kasar Sin ta taba gabatar da bayanai sama da 400 game da sayayyar Fentanyl ga bangaren Amurka.
Jagoran cibiyar nazarin manufar yaki da miyagun kwayoyi ta kasa da kasa ta kwalejin siyasa da tattalin arziki dake London ta kasar Birtaniya John Collins ya taba gaya wa manema labaran BBC cewa, ya dace a dauki matakin da ya dace domin dakile matsalar miyagun kwayoyin da Amurka ke fuskanta, a maimakon hana shigo da su daga ketare kawai.
Yanzu gwamnatin kasar Sin tana daukar Fentanyl a matsayin miyagun kwayoyi domin kiyaye kiwon lafiyar daukacin bil Adama, jami’in kasar Sin dake aikin yaki da miyagun kwayoyi Liu Yuejin yana ganin cewa, matakin da kasar Sin ta dauka zai hana masu aikata laifuffuka su tace sabon miyagun kwayoyi ta hanyar yin amfani da Fentanyl. A bayyane an lura cewa, matakin da kasar Sin ta dauka ya sake nuna wa kasashen duniya cewa, kasar Sin babbar kasa ce mai daukar nauyi bisa wuyanta a cikin harkokin kasashen duniya, musamman ma wajen yaki da miyagun kwayoyi, domin ya zama wajibi kasashen duniya su hada kai su kuma yi kokari tare yayin da suke yaki da miyagun kwayoyi a fadin duniya.

Exit mobile version