Za A kafa Dokar Zirga-zirgar Ababen Hawa Lokacin Zabe

Mukaddashin babban Sufeton ‘Yan sanda na kasa, Mohammed Adamu, ya yi umurni da a takaita zirga-zirgan ababen hawa tun daga karfe shida na safe zuwa shida na yammacin ranar Asabar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, (DCP) Frank Mba, ne ya fadi hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce an takaita zirga-zirgan ne saboda tsaron lafiyar al’umma, da tsaron kasa, saboda babban zaben da za a yi a ranar.
Mba ya ce, hakan zai taimaka wa jami’an tsaro wajen iya tabbatar tsaro a lokacin zaben, ta yanda hakan zai taimaka wajen magance duk wata tarzoma da kokarin watsa harkar zaben da batagari za su so haifarwa.
Ya bukaci ‘yan kasa da su yiwo fitan dango a ranar zaben domin sauke hakkin da ke kansu na jefa kuri’un su ba tare da tsoro ko shakkan komai ba, domin ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun dauki duk matakin da ya kamata a dauka wajen magance duk wani kalubale da samar da zaman lafiya.
Ya ce, “Muna jajantawa al’umma duk wani rashin jin dadin da daukan matakin hana zirga-zirgan zai haifar masu, babban Sufeton ‘yan sandan yana gargadin duk wani mai son kawo rudami a lokacin zaben da cewa rundunar ‘yan sandan ba za ta saurara ma shi ba.”
Ya kuma bukaci al’umma da su guji saye ko siyar da kuri’a, maganganun batunci, yada jita-jita, kwatan akwatunan zabe da aikata duk wani abin da ya sabawa doka.

Exit mobile version