Za A Karfafa Binciken Yadda Ake Kashe Kudaden Gwamnati

Don tabbatar bin ka’ida da kuma yakin da ake yi na cin hanci da rashawa a kasar nan, masu ruwa da tsaki a fannin binciken kudi sun yi kira a karfafa yadda ake yin binciken kudi a kasar nan. Sakataren Gwamnatin jihar Legas Mista, Tunji Bello a jawabin sa a taron karshen shekara karo na tara na fannin binciken kudi, ya yi nuni da cewa, akwai bukatar a karfafa tsare-tsaren binciken kudi na gwmnati don tabbatar da bin ka’ida wajen aiwatar da aikin gwamnatin Bello wanda ya sanar da hakan ta hanyar wakilin sa a wurin taron babban sakatare a ofishin gwamnan jihar Mista Adesina Odeyemi, ya cgi gaba da cewa, karfafa tsare-tsaren na binciken kudaden gwamnati zai bayar da kariya a kan yadda ake kula da kashe kudi. Acewar Mista Bello karfafa tsare -tsaren binciken kudade na gwamnati ya zama wajibi wajen gudanar da harkar mulki a cikin sauki hakan kuma zai baiwa hukumomin gwamnati kwarin gwaiwar inganta ayyukan su da kuma da gudanar da harkar mulki. Da yake yin tsokaci a kan 5aken taron, Fannin Binciken Kudi na Gwamnati, Mafita ga Shugabanci na gari da ibganta tattalin arzikin kasa, Bello ya shawarci ofishin Odita Janar na jihar ya samar da mataki na musayar bayanai da kuma sanya ido . Sakataren ya ce, mafi yawancin masu binciken kudi na gwamnati suna da dabi’ar mai-mai ta binciken da suka gudanar daga cikin takardun gargadi da aka basu a shekara. Acewar sa, ya zama wajibi mu kaucewa yin mai-maicin kuma dole ne mu kawo karshen hakan. Ya jadda cewa, ya zama wajibi masu bincikrn kudi na gwamnatin su rungumi ka’idojin da aka shinfida na binciken kudi don a karfafa fannin. Acewar sa, muna bukatar karfafa tsare-tsaren na binciken kudi na gwamnati,inda dole ne ayi aiki tare don sanya ido don a cimma burin da aka sanya a gaba da jihar ta tsara. Odita Janar ta jihar Legas uwargida Morenike Deile a nata jawabin a wurin taron tace, taken taron an zabo shi ne yadda masu binciken kudi zasu fuskanci kalubalen dake gaban su na karni. A karshe ta ce, an kuma dauko masu yin jawabin ne a wurin taron don ilimantar da masu binciken kudin da kuma karfafa ayyukan su.

Exit mobile version