Gwamnatin Tarayya ta kara wa’adin da aka diba wa ’yan Nijeriya don yin rajista da kuma danganta lambar shedar dan kasa ta (NIN) zuwa katin SIM dinsu kafin 9 ga Fabrairu, 2021
Wannan sanarwar tana kunshe ne a shafin Twitter na NIMC.
NIMC da farko ta bayar da wa’adin 19 ga Janairu ga wadanda ke da NIN sai kuma 9 ga Fabrairu ga wadanda ba su da NIN.
Kamar yadda sanarwar ta futo a twitter: “An shawarci dukkan ‘yan Nijeriya da masu bin doka da su yi rajistar lambar shaidar su ta ‘yan kasa (NIN) sannan su hada su kafin 9 ga Fabrairu, 2021.
Yi rijista don samun lambar shaidar ku ta ‘yan kasa (NIN) a yau !!!
“Da fatan za a tuna, rajistar NIN kyauta ce.”