Connect with us

LABARAI

Za A Sake Bude Ofishin Jakadanci Amurka Na Abuja

Published

on

Za a sake bude ofishin Jakadancin Amurka da ke Abuja a ranar 24 ga watan Agusta, domin masu neman biza da kuma yin hidima ga al’ummar kasar ta Amurka, bayan mako guda da rufe shi.

Ofishin ya jajanta wa masu hulda da shi kan dakatar da aikace-aikacen na shi na tsawon mako guda, cikin sanarwar da ofishi

n ya bayar a shafin sa na yanar gizo a ranar Litinin, ofishin ya ce, masu bukatar biza da makamantan hakan da aka bukaci da su zo a ranar Juma’a, yanzun suna iya zuwa ofishin kamar yadda aka saba.

“Duk masu bukatar biza da ‘yan Amurkan da aka nemi da su zo a tsakankanin ranakun 13 zuwa 23 ga watan Agusta ofishin zai tuntube su domin a ba su sabuwar ranar da za su zo.

Ofishin ya ce, “Wadanda suka nemi biza da ‘yan Amurkan da wani jami’in ofishin ya bukaci da su zo don amsa tambayoyi suna iya tuntuban ofishin don jin sabuwar ranar da aka ba su a wannan adireshin, ConsularAbuja@state.gob for bisas or AbujaACS@state.gob for ACS.

Ofishin kuma ya tabbatar wa da dukkanin wadanda suka mika Fasfo din su ta hanyar tattaunawar neman sake bizan za a duba lamarin na su cikin hanzari.

Ya kara da cewa, duk wadanda aka amince da na su za a aiko masu da sakonnin hakan ta adireshin su ba da jimawa ba.

“’Yan Amurka da ke Abuja da suke da bukatar Fasfo din su da aka rigaya aka kammala suna iya zuwa ranar Juma’a da karfe 9:30 zuwa 11:00 na safe. In kuma ba ka da tabbacin ko Fasfo din naka ya kammala ne kana iya tuntuban mu ta nan, AbujaACS@state.gob,”

A baya, ofishin ya bayar da sanarwar zai kulle ofishinsa na Legas a ranakun Talata da Laraba saboda bukukuwan Sallah.

Ofishin kuma ya gargadi duk ‘yan kasar ta Amurka da su yi taka-tsantsan a lokutan bukukuwan Sallah din, ya kuma yi nu ni da tsauraran matakan tsaro a bisa barazanar ‘yan ta’adda.

Ofishin ya ce, ‘yan Amurka din su tsammaci karin wuraren bincike na ‘Yan sanda da Sojoji a kan tituna, don haka duk inda za su je su tabbatar da suna tare da cikakkun takardun su na shaida da suka hada da Fasfo din su na Amurkan da kuma bizar su ta zama a kasar nan.

Ofishin kuma ya gargadi ‘yan Amurkan da su guji tafiye-tafiye a cikin dare, su kuma rage yawan yawace-yawace, da wuraren taruwar jama’a, su kula da duk na tare da su su kuma guji nu na kawukan su.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: