Abba Ibrahim Wada" />

Za A Samu Kamar Ronaldo Nan Gaba Kadan – Roberto Carlos

Ronaldo

Tsohin dan wasan Brazil da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Roberto Carlos, ya bayyana cewa nan gaba kadan duniya zata shaida dan wasa kamar Ronaldo saboda duniya ta canja ana samun manyan ‘yan wasa a duniya.

Carlos yayi wannan jawabi ne kwanaki kadan bayan da tsohon dan wasan Portugal, Luis Figo, ya bayyana cewa nan gaba ba za’a sake samun dan wasa mai hazaka kamar Cristiano Ronaldo ba sai bayan shekara hamsin.
Figo ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da manema labarai a babban birnin kasar ta Portugal wato Lisbon, bayan da akayi masa tambaya akan dan wasa Ronaldo da kuma irin tarihin daya kafa a duniya duk da cewa har yanzu baiyi ritaya daga buga kwallo ba.
Carlos, wanda yayi hira da wani gidan Radio a Brazil ya bayyana cewa duniya tana canjawa kuma ana samun matasan ‘yan kwallo masu hazaka da sha’awar wasan kwallo saboda haka ba za’a dauki lokaci ba kafin a samu kamar Ronaldo.
A tsakiyar watan jiya ne Cristiano Ronaldo ya ci kwallonsa ta 760 a duniya a wasan Super Coppa na kasar Italiya da Jubenstus ta samu nasara da ci 2-0 a kan kungiyar Napoli, abin da ya sake tada ikirarin cewa shi ne dan kwallon da ya fi saka kwallaye a raga a duniya sai dai akwai takaddama a kan waye ya fi cin kwallaye a duniyar har yanzu.
Ronaldo ya fara nuna bajinta, inda a matsayinsa na matashin dan wasa, ya ci wa tsohuwar kungiyarsa ta Sporting Lisbon kwallaye 5, sannan daga baya  ya koma Manchester United ya ci kwallaye 118, bugu da kari ya ci kwallaye 450 a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, sannan sai kwallaye 85 a Jubentus, sai kuma guda 102 a tawagar kwallon kafar kasar sa ta Portugal.
dan wasan gaban na tawagar kwallon kafar Portugal, wanda a wata mai kamawa zai cika shekara 36 a duniya ya kafa tarihi a harkar kwallon kafa a bangarori da dama domin shi ne dan wasan da ke kan gaba a cin kwallaye a Real Madrid da kuma kasarsa, kuma yana gaban dan wasa Lionel Messi a cin kwallaye a gasar zakarun nahiyar Turai.
Sai dai ana ci gaba da kokwanto a kan ko Ronaldo din ne ke kan gaba a harkar kwallon kafa gaba daya wajen yawan kwallaye, saboda ‘yan wasan Brazil Pele da Romario na ikirarin cewa sun ci sama da kwallaye dubu daya a rayuwarsu.
“za’ayi shekara 50 ba’a sake samun dan wasa kamar Ronaldo ba idan muka kalli matasan ‘yan wasan da akeyi yanzu a duniya amma bance duniya ba zata sake ganin dan wasa kamar Ronaldo ba sai dai wanda zaiyi abinda yayi tabbas za’a dade”  a cewar Figo
A watan Disambar daya gabata Lionel Messi ya zarta kwallaye 643 da aka amince da su a hukumance cewa Pele ya ci wa kungiya guda, amma ba tare da bata lokaci ba kungiyar Santos ta Brazil, wadda Pele ya yi wa wasa suka ce gwarzon dan kwallon da ya lashe kofin duniya har sau uku ya ci musu kwallaye dubu daya da 19 idan aka hada da wasannin sada zumunta.
Bayanin Pele a shafinsa na Instagrm na nuni da cewa shine ya fi kowa saka kwallaye a raga a harkar kwallon kafa a duniya, da kwallaye dubu daya da dari biyu da 83 sai dai kuma, idan wasanni da aka yi a hukumance ne abin la’akari, dan kasar Brazil din, wato Pele, yana bayan Josef Bican, wanda masana tarihin kwallon kafa suka yi ittifakin cewa ya ci kwallaye 805 a cikin wasanni 530 a tsakanin shekarun 1931 da 1955, inda ya buga wa kungiyoyi 6 da kuma kasashen Austria da Czechoslobakia.
Pele ya ci kwallaye tsakanin 757 da 767 a wasannin da ya yi a sana’arsa ta kwallon kafa da suka hada da 92 da ya ci wa kasarsa Brazil sannan an sanya shi a matsayin na uku a bayan wanda ya taimaka wa Brazil a gasar kofin Duniya ta shekarar 1994 mai kwallaye 772 Romario.
A shekarar 2007 Romario ya yi bikin kai wa kwallaye dubu daya, adadin da ya hada da kwallayen da ya ci tun yana matashin dan wasa da kuma wasannin sada zumunta da na karramawa.
Shi ko Messi, wanda shekarunsa 33 yana da kwallaye 719 wadanda ya ci wa Barcelona da Argentina kuma yana iya cimma ma wadanda ke gabansa kafin ya yi ritaya saboda har yanzu yana buga kwallo.
Sai dai abin da ake kyautata zato a nan shi ne, ko da Ronaldo bai kafa tarihin zama dan wasan da ya fi kowa zura kwallo a raga ba a yanzu, akwai alamun cewa zai cimma haka a matsayinsa na dan wasan da ke ci gaba da cin kwallaye duk da cewa yana daf da cika shekaru 36 da haihuwa.

Exit mobile version