Aabubakar Abba">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home NOMA

Za A Samu Karancin Waken Soya A Bana, Cewar Manoma

by Aabubakar Abba
December 3, 2020
in NOMA
3 min read
Waken Soya

WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Wasu daga cikin manoman waken soya a jihohin Benuwe, Katsina, Zamfara da kuma Jihar Kaduna sun bayyana cewa, fari ya janyo za a samu karancin waken soya a bana.

Sai dai, manoma da sauran masana harkar noma sun ambaci wasu dalilai, kamar tsadar kayan masarufi, rashin samun takin zamani a kan lokaci kullen korona da sauransu, inda suka kara da cewa, tsawon farin da aka fuskanta a watan Agusta shi ne babban kalubalen a fannin.

samndaads

An ruwaito cewa, a jihar Benuwe a wani bangare manoma sun bayyana cewa, rashin amfanin gonar na iya haifar da karancin amfanin gona a lokacin kaka.

Masu ruwa da tsaki na fargabar cewa kasar nan na iya fuskantar hauhawar farashin waken soya a watannin da ke tafe saboda raguwar kayan, inda kuma an kuma lura cewa duk wani karancin waken soya zai yi mummunan tasiri a kan farashin abincin dabbobi, musamman a masana’antar kiwon kaji.

Dakta Hassan Dalha wanda kuma shi ne ma’aji na kungiyar manoman waken Suya na na kasa ya kara da cewa, a jihohin Katsina, Zamfara da Kaduna, manoma da yawa ba su shiga harkar noma saboda ayyukan ‘yan fashi.

A cewar Dakta Dalha, wanda ke noman waken soya a lokacin damina da lokacin rani, ya bayyana dalilin da ya sa dole ne kasar ta dage don kwanaki masu wuya da ke tafe.

Shi ma wani manomi da baya son a ambaci sunansa ya kuma ce cutar ta korona ta shafi samar da kayayyaki kasancewar an takaita zirga-zirga don’t a dakike yaduwar cutar a kasar nan.

A cewarsa, a wannan lokacin, manoma da yawa ba sa iya samun damar shiga gonakinsu ko kuma samun leburori da za su yi musu aiki, inda ya kara da cewa, amfanin gonar ya kan dauki kwanaki 120 zuwa 140 kafin girbi.

Ya kuma lura da cewa Babban Bankin Nijeriya (CBN), a karkashin shirin aikin noma na Anchor Borrowers, bai fitar da kudi ga kungiyar ba a kan lokaci domin noman bana, inda ya ce, kungiyar ta kama bayanan manoma a kusan jihohi 18 daga cikin 36 na tarayyar, tare da sama da manoma 20 rajista.

Ya kuma kara da cewa, idan kuna da manoma sama da dubu 20 kuma ba su cikin jirgi, za ku sami kari ko ragi, inda ya jero wasu dalilai, Dakta Dalha ya kuma nuna gaskiyar cewa kayan masarufi ba su isa ga manoma a kan lokaci, lamarin da ya ce ya shafi da yawa daga cikinsu, inda ya yi tir da tsadar kayan masarufi, wanda ke karya gwiwar mutane da yawa daga noman waken soya.

Bugu da kari, an kuma ruwaito cewa, manoma a yankunan Keana da Kanje da ke Jihar Nasarawa an bayyana cewa, da yawa daga cikinsu sun yanke shawarar barin waken soya don’t komawa noman shinkafa.

Wani manomi a garin Ogobia a karamar hukumar Otukpo a jihar Benuwe, Fasto Sunday Okopi, ya ce matsalar fari ta fara bayyana ne a lokacin noman, inda ya kara da cewa, akwai fari a lokacin da ya kamata mu shuka waken soya hakan ya kuma ya dade har zuwa karshen watan Agusta.

Ya cigaba da cewa, bayan wannan, wadanda muka dasa ba za su iya yin kyau ba har ya zuwa lokacin nan da muke magana, har yanzu suna fure, ya ci gaba da cewa, lokacin da muka fahimci abin da zai faru, mun sadaukar da yawancin filayen ga wake kuma mun yi amfani da kadada uku na waken soya, wanda ba a samu nasara ba.

Okopi ya ce, ya shuka mafi kyawu, wanda aka fi sani da 1448, wanda ya shahara, har ma a tsakanin sauran manoman waken soya a Yankin Mazabar Benue ta Kudu, inda ya kara da cewa, rashin isasshen ruwan sama ya shafi shuka.

Ya nuna tsoron cewa farashin waken soya, wanda tuni ya tashi a wannan lokacin noman girbi, idan aka kwatanta shi da na bara, zai kara tabarbarewa zuwa shekara

SendShareTweetShare
Previous Post

Babu Gwamnati Da Rabon Kudinta Ya Je Hannun Talaka Kamar Ta Buhari – Dikko Radda

Next Post

Kamfanin Farmcrowdy Ya Gudanar Da Bikin Shekaru Hudu

RelatedPosts

Noman Kashu Na Taimaka Wa Fannin Tattalin Arziki, Cewar NCAN

Noman Kashu Na Taimaka Wa Fannin Tattalin Arziki, Cewar NCAN

by Aabubakar Abba
4 hours ago
0

kungiyar masu noman Kashu ta kasa (NCAN) ta yi kira...

Shirin Aikin Noma Na LIFE-ND Zai Inganta Rayuwar Mazauna Yankin Neja-Delta – Minista

Shirin Aikin Noma Na LIFE-ND Zai Inganta Rayuwar Mazauna Yankin Neja-Delta – Minista

by Aabubakar Abba
4 hours ago
0

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa, za ta kashe akalla...

Dalilinmu Na Noma Tumbar Kadada 15,000 Na Roba A Kuros Ribas – NARPPMAN

Dalilinmu Na Noma Tumbar Kadada 15,000 Na Roba A Kuros Ribas – NARPPMAN

by Aabubakar Abba
5 hours ago
0

Akwai alamun dake nuna cewa, akwai fata nagari a fannin...

Next Post
Kamfanin Farmcrowdy

Kamfanin Farmcrowdy Ya Gudanar Da Bikin Shekaru Hudu

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version