Za A Samu Karin Matalauta Miliyan 20 A Nijeriya Nan Gaba Kadan

Nijeriya tana bukatar gagaruman garanbawul a bangaren tattalin arziki a yanzu, kafin ta

samu nasarar ceto ‘yan kasar daga matsanancin talauci, kamar yadda mashawarcin

shugaban Bankin Duniya ta fannin tattalin arziki, Doyin Salami, ya bayyana, yana mai cewa,

nan gaba kadan za a samu karin matalauta a kasar daga miliyan 15 zuwa 20.

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wajen taron farfado da tattalin arzikin Nijeriya ta

hanyar yadda za a yi tunanin kawo dangantaka da kamfanoni masu zaman kansu, domin

magance matsalar.

A wajen taron, Bankin Duniya ya bayyana ya kiyasta cewa, za a samu ‘yan Nijeriya tsakanin

miliyan 15 zuwa miliyan 20 wadanda za su fada cikin talauci daga nan zuwa shekarar 2022.

Babbar masaniyar tattalin arziki na Bankin Duniya, Gloria Joseph-Raji ta bayyana cewa, cutar

Korona ta ingiza tattalin arzikin Nijeriya cikin mawuyacin halin a shekarar 2020, wanda bai

taba shiga matsi irin wannan bat un wanda aka taba samu a shekarar 1980. A cewata, akwai

bukatar Nijeriya ta gaggauta samar da tsare-tsare wasu manufofi wadanda za su taimaka

wajen inganta harkokin kasuwanci da kuma bunkasa walwalan ‘yan Nijeriya.

Ta ce, “a zahirin gaskiya muna duba halin da Nijeriya take cikin a yanzu duk ta tana da tsarin

da ta saka a gaba wajen tsamo da mutane miliyan 100 daga kangin talauci kafin shekarar

2030, wanda aka fara gudanar da shirin tun kafin zuwan cutar Korona, lokacin da cutar

Korona ta kunno kai ta dagula lissafi wanda a yanzu ne ma aka fi bukatar wannan shiri cikin

gaggawa.

“Bisa yadda ake samun nakasu da karuwar marasa aikin yi da hauhawan farashin kayayyaki,

mun kiyasta cewa yawan ‘yan Nijeriya za sa kara fadawa cikin talauci za su kai tsakanin

mutane miliyan 15 zuwa 20 kafin shekarar 2022, wanda ya zarce mutane miliyan 83 da ake

da su a shekarar 2019.”

Joseph-Raji ta kara bayyana cewa, akwai bukatar mahukuntan kasa su gudanar da garan

bawul wanda zai magance matsalar. Ta ce, kamata su yi kokarin amince da kyakkyawn tsarin

kasuwanci farashin man fetur da na wutar lantarki wajen dai-daita hanyoyin kudade.

“Haka kuma, akwai bukatar Nijeriya ta gudanar da taron gaggawa cikin cimma matsaya a

kan bunkasa tattalin arziki,” in ji ta.

A cewar Joseph-Raji, mahimman abubuwan da gwamnatin Nijeriya za ta mayar da hankali

dai sun hada da amincewa da kasuwancin kasa da kasa da inganta hanyoyin haraji wadanda

ba za su raunata harkokin zuba jari da samar da manufofin kudade wanda za su dai-dai

farashi. Ta ce, bayan dukkan wadannan abubuwa, akwai bukatan Nijeriya ta gudanar da

garan bawul da zai farfado da harkokin tattalin arziki.

A nasa bangaren, Salami ya bayyana cewa, akwai bukatar kasar ta zuba jari mai yawa domin

su cimma manufar tattalin arziki.

Ya ce, “idan akwai ci gaban tattalin arziki, mutane za su ji a jikinsu wanda ba za a sami jin

dadi da walwala. Mun yi matukar tsintan kanmu a cikin mummunan yanayin tattalin arziki

wanda ya kai na kashi shida wanda muke bukatar zuba jari.”

Kasa da shakara daya kenan, ana fama da matsin tattalin arziki wanda ba a taba gani ba tun

shekaru biyar da suka gabata sakamakon cutar Korona.

Salami ana samun matsin tattalin arziki a duniya, amma ba irin wanda Nijeriya take ciki ba

wanda take bukatar agajin gaggawa na musamman.

Exit mobile version