Daga Rabiu Ali Indabawa
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a yau Alhamis za ta saurari neman belin Sanatan Borno ta Kudu, Alhaji Ali Ndume.
Ndume ya kasance a tsare a gidan yari tun ranar Litinin saboda tsaya wa tsohon Shugaban rusasshiyar kungiyar fansho da aka yi wa garambawul, Abdulrasheed Maina, wanda ake ganin ya tsallake sharudan beli.
Maina na fuskantar tuhumar almundahanar kudi da ta shafi Naira biliyan 2 kafin a ba da belinsa.
Alkalin, a yayin shari’ar da babu Maina, a ranar Laraba, ya amince da bukatar belin da lauyan Ndume ya shigar. Ya ce an kawo masa bukatar belin ne da misalin karfe 8.58 na safiyar ranar Laraba, inda ya bayyana cewa nan take ya bayar da umarnin a tsayar da batun don sauraron karar a yau Alhamis.
Ya kuma ce ya bayar da umarnin cewa a bayar da sanarwar sauraren karar a yau Alhamis kuma a ba wa bangarorin. Duk da cewa lauyan Ndume bai halarci kotun ba, amma lauyan EFCC, Mohammed Abubakar, ya tabbatar da cewa an kawo masa sanarwar sauraren karar.