Gwamnatin tarayya ta bude sabon shafin da zai taimakawa tsaffin matasan N-Power daman neman tallafi da jari na babban bankin Nijeriya CBN.
Wannan shafi da ma’aikatar jinkai da walwala ta shirya tare da hadin kan CBN zai taimakawa wadanda aka cire daga shirin N-Power su shiga domin neman abubuwan alfanu da CBN ke da shi na tallafi, bashi da jari.
A jawabin da Sakataren ma’aikatar, Bashir Nura Alkali ya sake a madadin ministar, Hajiya Sadiya Farouq, ta yi kira ga matasan su shiga shafin domin sanya sunayensu saboda su samu shiga cikin duk wani shiri da CBN za ta gabatar.
“An bude shafin NEXIT ne domin ganin inda matasan N-Power zasu samu shiga a shirye-shiryen CBN kuma sai mutum ya cika sharrudan wadannan da CBN ta kindaya,” cewar Minista Sadiya.
Ministar ta mika godiyarta ga gwamnan CBN, Godwin Emefiele kan wannan taimako.
Hajiya Sadiya ta yi alkawarin cewa ma’aikatarta za ta cigaba da hada kai da wasu ma’aikatun gwamnati da masu ruwa da tsaki wajen ganin an cimma manufar shugaba Buhari na tsamo mutane milyan 100 daga cikin talauci.